Ba za zamu kara wa ma’aikata albashi ba bai – el-Rufa’i
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufa’i ya bayyana cewa ba za a yi wa ma’aikatan jihar karin albashi ba a cikin kasafin kuin bai har sai kuin shiga na harajin jihar sun karu. Ya ce su ma manyan jami’an gwamnati za a rage kuin alawus insu a matsayin sadaukar da kai ga canji da aka […]
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufa’i ya bayyana cewa ba za a yi wa ma’aikatan jihar karin albashi ba a cikin kasafin kuin bai har sai kuin shiga na harajin jihar sun karu.
Ya ce su ma manyan jami’an gwamnati za a rage kuin alawus insu a matsayin sadaukar da kai ga canji da aka samu.
Gwamnan ya sanar da haka ne a lokacin da ya gabatar da kasafin kui na shekara 2016 ga jama’a da sauran masu ruwa da tsaki kafin a mika wa majalisar jihar domin amincewa da shi. Ya ce hatta alawus na tafiye-tafiye na jami’an gwamnati duk za a rage su.
Naira biliyan 166 ne kasafin kuin da gwamnan ya kaddamar na shekarar mai zuwa. “Ba za mu kara wa ma’aikata kuin albashi ba a cikin kasafin kuin bai har sai kuin harajinmu ko kuin shiga a jihar sun karu. Haka su ma jami’an gwamnati za a rage masu alawus da kuin tafiye-tafiye a matsayin sadaukar da kai ga canji da aka samu.”
Ya kuma tabbatar wa jama’ar jihar cewa gwamnatinsa za ta samar da shirye-shiryen da za su taimaka wajen ciyar da yara a makarantu, shuka bishiyoyi da za su taimaka wajen inganta tattalin arziki da sauransu.
A cewarsa, shirye-shiryen da gwamnatinsa ta sanya cikin kasafin kuin za su taimaka wajen samar da akalla ayyuka sama da dubu 200 ga al’ummar jihar.