Ba zai yiwu APC ta gyara barnar PDP cikin wata 10 ba – Gwamna Abubakar

Gwamnan Jihar  Bauchi, Mohammed Abubakar ya bukaci ’yan Najeriya su rage dimbin bukatun da suke fatar samu daga gwamnatin Jam’iyyar APC, inda ya ce jam’iyyar ba za ta iya yin dabo ta gyara komai cikin dare daya ba.Gwamna Abubakar ya fadi a tattaunawa da wata jarida cewa Jam’iyyar PDP ta shafe shekara 16 tana tafka […]

Ba zai yiwu APC ta gyara barnar PDP cikin wata 10 ba – Gwamna Abubakar
Ba zai yiwu APC ta gyara barnar PDP cikin wata 10 ba – Gwamna Abubakar

Gwamnan Jihar  Bauchi, Mohammed Abubakar ya bukaci ’yan Najeriya su rage dimbin bukatun da suke fatar samu daga gwamnatin Jam’iyyar APC, inda ya ce jam’iyyar ba za ta iya yin dabo ta gyara komai cikin dare daya ba.
Gwamna Abubakar ya fadi a tattaunawa da wata jarida cewa Jam’iyyar PDP ta shafe shekara 16 tana tafka barnar da APC ke kokarin gyarawa, kuma ya ce zai zamo kuskure a dora wa gwamnatin APC wadda ba ta kai wata goma ba laifin halin da kasar nan take ciki a yanzu.  
“Ba a yi wa gwamnatin APC adalci a dora mata laifi. Mutane sun mance PDP ta shafe shekara 16 tana mulki. Don haka kada mutane su tsammaci dabo daga APC. Muna sadaukar da kai. Za ku gani daga lokacin da muka karbi mulki, ko man fetur wanda farashinsa ya fara faduwa ya fara tashi a yanzu sakamakon kokarin Shugaban kasa. Don haka mutane su kara hakuri. Ya kamata mutane su ba mu akalla shekara 16 don su ga ko ba za mu iya gyara barnar da PDP ta shuka ba. Bai dace ’yan Najeriya su dora mana laifin gazawa a kasa da wata takwas zuwa tara ba. Ina ba ’yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatin APC a matakin tarayya tana kokari, haka gwamnatocin APC a jihohi za su yi rawar gani insha Allahu,” inji shi.
Gwamna Abubakar ya ce irin tabargazar da aka tafka a Jihar Bauchi ne ta tilsta shi ya binciki gwamnatin da ta gabata domin kwato dukiyar da maciya amana suka wawure. Ya ce zuwa yanzu kwamitin da gwamnatin ta kafa ya kwato dukiya  mai yawa tare da gano ma’aikatan bogi dubu 19 a jihar.
Gwamna Abubakar ya ce al’ummar jihar sun cancanci su san yadda ake tafiyar da harkokinsu. “Muna bincikar gwamnatin da ta gabata kuma an bankado abubuwa da dama zuwa yanzu. Yanzu haka ina da kwamiti mai karfi da yake bincikar dukkan kwangilolin da aka bayar daga shekarar 2007 zuwa 2015. Wannan bayan na kafa kwamitin kwato dukiyar gwamnati a karkashin shugabancin wani Kwamandan Sojin Sama wanda ya samu nasarar kwato dimbin kadarorin gwamnati da aka sace,” inji Gwamnan.  
Ya ce an gano ma’aikatan bogin ne bayan gwamnatinsa ta nace wajen yin amfani da lambar tantancewa asusun ajiyar banki domin gano hakikanin ma’aikatanta.
Gwamna Abubakar ya ce ya zama wajibi ya dakatar da biyan albashi ta hanyar biyan kudi kai-tsaye, kuma ya ce daga Fabrairun bana duk ma’aikatan gwamnatin jihar da na kananan hukumomi za su karbi albashinsu ne ta wasu bankuna da aka kebe.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta yi amfani da rahoton binciken kwamitin wajen kiran Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta gurfanar da wadanda aka samu da hannu tare da kwato dukiya da kadarorin da suke hannun wasu daidaikun mutane.