Ba zai yiwu mu bar Khamenei a raye ba — Isra’ila
Kafin harin an yi ƙoƙari kwashe marasa lafiya da dama, saboda a ceto rayukansu.
Khamenei
Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz ya ce ba zai yiwu su bar jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei a raye ba.
Israel Katz ya yi barazana ga Ayatollah yana mai cewa ya zama tilas ya ɗauki alhakin hare-hare da makamai masu linzami da Iran ta yi a kan wata cibiyar lafiya da ke kusa da Tel Aviv.
- Hisbah ta lalata katan 243 na barasa da wasu kayan maye a Yobe
- Guguwar ruwan sama ta yi ɓarna a Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Kogi
Kafin harin an yi ƙoƙari kwashe marasa lafiya da dama, saboda a ceto rayukansu.
Tuni dai Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ziyarci Cibiyar Lafiya ta Soroka da ke Beersheba da harin makami mai linzami na Iran ya faɗawa.
Sai dai ita kuma Iran din ta ce ta kai harin ne kan sansanin sojoji da ke kusa da asibitin.
Kalaman Mista Katz na nuna cewa sojojin Isra’ila a yanzu za su yi ƙoƙarin ganin sun kashe Ayatollah — bayan kashe kwamandojinsa na soji da dama.
A makon da ya gabata ne Isra’ila ta ƙaddamar da hare-hare ta sama kan babbar abokiyar gabarta a yankin Gabas ta Tsakiya Iran, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar manyan kwamandojin sojin ƙasar, tare da lalata wasu cibiyoyin nukiliyata da kuma kashe fararen hula da dama.