Ba zamu janye shirin fara yajin aikin gama gari ba – ASUP

Kungiyar malaman kwalejin kimiyya ta Najeriya ASUP a yau Talata ta ce, babu ja da baya akan shirin su na fara yajin aikin gama gari daga gobe 12 ga Disamba 2018, a duk makarantun kasar. Shugaban kungiyar na kasa Mista Usman Dutse, ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai NAN a jihar Legas. Dutse […]

Ba zamu janye shirin fara yajin aikin gama gari ba – ASUP

Kungiyar malaman kwalejin kimiyya ta Najeriya ASUP a yau Talata ta ce, babu ja da baya akan shirin su na fara yajin aikin gama gari daga gobe 12 ga Disamba 2018, a duk makarantun kasar.

Shugaban kungiyar na kasa Mista Usman Dutse, ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai NAN a jihar Legas.

Dutse ya ce, fara yin yajin aikin ya zama wajibi samakon rashin cika alkawarin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi a shekarar 2009 da 2017 tsakaninsu da kungiyar.