Ba zamu kori manyan jami’an tsaro yanzu ba: Fadar Shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani akan kiraye-kirayen da ake ta yi wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, na ya kori manyan jami’an tsaron kasa duba da tabarbarewar al’amuran tsaro a kasar, fadar shugaban kasar ta bayyana cewa ba zata kori manyan jami’an tsaron ba a daidai wannan lokacin. Sakataren Gwamnatin tarayyar Najeriya Boss Mustafa, […]

Ba zamu kori manyan jami’an tsaro yanzu ba: Fadar Shugaban kasa

Manyan jami’an tsaron Najeriya

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani akan kiraye-kirayen da ake ta yi wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, na ya kori manyan jami’an tsaron kasa duba da tabarbarewar al’amuran tsaro a kasar, fadar shugaban kasar ta bayyana cewa ba zata kori manyan jami’an tsaron ba a daidai wannan lokacin.

Sakataren Gwamnatin tarayyar Najeriya Boss Mustafa, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a sa’ilin da ya halarci taron kaddamar da littafi a birnin tarayya Abuja.

Ya ce, ba a korar manyan jami’an tsaron haka kawai, “Akwai matakan da ake bi wajen yin hakan, kana na tabbata idan lokaci ya yi za abi matakan, ba za a wayi gari lokaci guda a kori manyan jami’an ba.” In ji shi.

Ya kamata Buhari ya kori manyan jami’an tsaron kasa – Kadariya Ahmed

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa