Ba zan ba ’yan adawa dama su mulki Najeriya ba – Jonathan

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya ce gwamnatinsa ba za ta ba ‘yan hamayya dama su mulki Najeriya ba. Shugaba Jonathan ya bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin da yake kaddamar da wani shirin kamfe mai suna PDP Wards’ bolunteer Scheme a fadar Shugaban kasa da ke Abuja da nufin shiga lungu da sako […]

Ba zan ba ’yan adawa dama su mulki Najeriya ba – Jonathan
Ba zan ba ’yan adawa dama su mulki Najeriya ba – Jonathan

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya ce gwamnatinsa ba za ta ba ‘yan hamayya dama su mulki Najeriya ba.

Shugaba Jonathan ya bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin da yake kaddamar da wani shirin kamfe mai suna PDP Wards’ bolunteer Scheme a fadar Shugaban kasa da ke Abuja da nufin shiga lungu da sako da mutum miliyan daya za su sadaukar da kai.
Ya zargi wasu mutane da bai fadi sunansu ba, da caccakar gwamnatinsa cikin “damuwa da bacin rai da kuma rashin gaskiya.”
Ya ce: “Na sha fadi cewa idan ka ga mutane suna magana zuciyarsu na tafasa ka ga damuwa da bacin rai, ka dauke su mutanen da suke cike da laifi, idan ba ka da zuciyar yafiya, ba ka da zuciya mai tsarki, ba za ka mulki Najeriya ba, domin ba za ka iya bayar da abin da ba ka da shi ba.”
Shugaba Jonathan ya ce PDP ta kafa tsari na shugabanci da abokan adawa ba za su iya gasa da ita ba, saboda ba su taba kafa gwamnati a matakin tarayya. “A matakin jiha da matakin tarayya; hakika a matakin tarayya ba za mu hada ingancinmu da nasu ba, ba su taba kafa gwamnati ba, don haka ba za mu ba su dam aba. Kuma na san ba za su iya abin kirki ba,” inji shi.
Ya ce, Jam’iyyar PDP ce kawai take da mambobi a kowace rumfar zabe, inda ya nuna damuwa kan yadda shugabanni da mambobin jam’iyyar ba su tallata nasarorinta. “Idan ka dubi bangaren aikin gona da na sufuri da na ilimi da na man fetur mun fadada wadannan sassa ta yadda suka bayar da dama ga manyan ‘yan Najeriya da ke bangaren aikin mai.”
Tun farko shugaban kwamitin dattawan Jam’iyyar PDP, Cif Tony Anenih ya nanata bukatar karfafa jam’iyyar a dukkan matakai.
Darakta Janar na kamfe din Jonathan Ahmadu Ali ya bukaci dukkan ‘ya’yan jam’iyyar su yi aiki tare don fuskantar zaben 28 ga Maris da 11 ga Afrilu.
Ahmadu Ali ya ce wasu kasashe da ya bayyana da tsofaffin abokan Najeriya suna adawa da sake zaben Jonathan ne saboda dokar haramta auren jinsi, inda ya ce Najeriya tana da al’adunta da ya kamata ta kare. Ya ce, “Ba mu damu da abin da tsofaffin abokanmu za su ji ba, saboda mun amince da dokar haramta auren jinsi. Mu kasa ce main al’adu, muna da tsarin al’adunmu. Mun yanke shawarar bin su, kuma dukkan Afirka suna dubi ne zuwa gare mu. Dimokuradiyya ba za ta zama daidai a wurin dukkan al’adu ba, kowace kasa za ta fassara ta ce gwargwadon al’adunta ta yadda za ta dace da fahimtarta. Don haka a ce abin da ke faruwa a can tilas ya faru a nan kuskure ne. Don haka za mu yi dimokuradiyya ne gwargwadon fahimtarmu kuma abin da muke yi ke nan. Muna iya kuskure, su ma da suka shekara 200 suna yi amma har yanzu suna kuskure.”
Ali ya ce an bullo da shirin ne domin gabatar da wani sabon fasalin kamfe na shiga cikin lungunan karkara. Ya bukaci mambobin jam’iyyar su yi aiki don samun nasarar Jonathan, inda ya ce a zango na biyu na Shugaban kasar ba za a yi watsi da wadanda suka yi masa hidima ba.