Ba Zan Bai Wa Wani Ɗana Shawarar Zama Soja Ba — Matar Laftanar Kanar Ali

Na tsinci kaina a cikin wani yanayi na tashin hankali bayan samun labarin rasuwar mijina.

Ba Zan Bai Wa Wani Ɗana Shawarar Zama Soja Ba — Matar Laftanar Kanar Ali

Matar marigayi Laftanar Kanar A.H Ali da wasu suka yi wa kisan gilla a kan hanyarsu ta kwantar da tarzoma a Karamar Hukumar Ughellin Jihar Delta ta ce ba za ta bai wa wani danta shawarar zama sojan Najeriya ba.

Laftanar Kanar A.H Ali jagoran rundunar sojin Najeriya ta 181 da ake kira da “Amphibious Battalion” a jihar Delta ya gamu da ajalinsa ne ranar Alhamis 14 ga Maris, 2024. 

Matar marigayin, Hauwa A.H Ali, ta ce ta kaɗu sosai da samun labarin rasuwar mijinta a daidai wannan lokaci. 

Ta ce, “Ya kira ni ranar da abin zai faru ya ce, za su je kwantar da tarzoma a wani gari. Ban san cewa hirar bankwana muka yi ba.

“Tun ranar Alhamis ɗin da abin ya faru, ba a samu wanda ya iya sanar da ni ba, sai ranar Asabar aka kira ni daga fadar shugaban kasa aka faɗa min.”

Hauwa A.H Ali a tattaunawarta da abokin aikinmu ta bayyana cewa, ta tsinci kanta a cikin wani yanayi na tashin hankali bayan samun labarin rasuwar mijinta. 

Ta ce “mu musulmi mun yarda da cewa za mu mutu, zamu koma ga Allah amma banji daɗin yadda aka kashe min mijina ba”

“Mijina jajirtacce ne, mai ƙwazo da ba da lokacinsa da ƙwarewarsa ga aikinsa, duk lokacin da aka neme shi a shirye yake ya ba da gudunmawarsa, ya sadaukar da rayuwarsa ga Najeriya.”

Dangane da batun ko za ta so wani danta ya gaji mahaifinsa, ta ce, “Ba zan bai wa wani dana shawarar zama sojan Najeriya ba, mahaifinsu ya yi duk abin da ya dace, ya sadaukar da jininsa ga ƙasarsa.”

Kisan rundunar ta Laftanar Kanar A.H Ali dai ta tayar da hankalin ’yan Najeriya, inda ake ta kiraye-kirayen dole a gaggauta bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki. 

An kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakin ba sani ba sabo kan duk wanda aka samu da hannu cikin aikata wannan mummunar ta’asa. 

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar 14 ga watan Maris ne wasu ɓata-gari suka hallaka sojojin kasar kimanin 16, waɗanda ke aikin wanzar da zaman lafiya a Karamar Hukumar Ughelli ta Kudu bayan barkewar rikicin kabilanci da kuma na mallakar kasa tsakanin kabilar Okuama da Okoloba a Jihar Delta.