Ba zan bar ’ya’yana su yi bara ba – Mahaifin makafi uku

Da ka isa kauyen Piko-Panda kafin ka shiga cikin garin za ka hango wani gidan kasa mai dakuna biyu a gefe. Nan ne gidan Malam Adamu Audu, inda yake zaune da matansa biyu da ’ya’yansa 16. Uku daga cikin ’ya’yansa, Shehu da Amina da Musa duk makafi ne da aka haife su da makanta. Duk […]

Ba zan bar ’ya’yana su yi bara ba – Mahaifin makafi uku
Ba zan bar ’ya’yana su yi bara ba – Mahaifin makafi uku

Da ka isa kauyen Piko-Panda kafin ka shiga cikin garin za ka hango wani gidan kasa mai dakuna biyu a gefe. Nan ne gidan Malam Adamu Audu, inda yake zaune da matansa biyu da ’ya’yansa 16. Uku daga cikin ’ya’yansa, Shehu da Amina da Musa duk makafi ne da aka haife su da makanta.

Duk da cewa Malam Adamu Audu bai yi karatun boko ba, amma duk da haka ya sanya ’ya’yan nasa uku makafi a Makarantar Makafi ta Abuja don su samu ilimin zamani.  daya daga cikin ’ya’yan mai suna Shehu yana aji daya ne a Makarantar Sakandare kuma yanzu yana da shekara 17, yayin da Amina mai shekara 11 take aji uku a firamare sai Musa mai shekara bakwai da yake aji daya a firamare a Makarantar Makafin da ke Unguwar Jabi a Abuja.
Shehu da Amina da Musa dukkansu sun bayyana burin zama malamai don su koyar da makafi ’yan uwansu. “Idan mun kammala karatu muna son zama malamai don mu ma mu bayar da tamu gudunmawar wajen yada ilimi ta hanyar koyar da makafi irinmu don su ma su samu ilimi mai inganci,” inji su.
Malam Adamu wanda ya haura  shekara 50 ya shaida wa Aminiya cewa bai taba barin ’ya’yansa sun yi bara ba, duk da talauci da yake fama da shi, saboda yadda bara take kashe zuciyar dan Adam tare da zubar masa da kima a idon jama’a.
Ya ce ya yanke shawarar sanya ’ya’yansa uku makafi a makarantar ne bayan duk kokarin da ya yi na nema musu magani ya ci tura.
Ya ce, “Dukkansu da makanta aka haife su. Na kai su asibitoci daban-daban tare da taimakon wani dan kabilar Ibo mai suna Augustine da ke zaune a kauyen Igu, amma likitoci suka fada mana cewa ba za su warke ba tun da haka Allah Ya halicce su.”
Sai dai kuma Malam Adamu ya ce bai taba sanin makaho zai iya samun ilimin zamani ba har sai da Augustine ya sanar da shi.“Ni gaskiya ban taba sanin makaho zai iya samun ilimin zamani ba, sai wata rana wani dan kabilar Ibo mai suna Augustine ya zo har gida ya same ni ya bayyana mini cewa ya kamata in kai ’ya’yana makaranta. Ni kuwa sai na ce masa ta yaya za a yi makaho ya iya rubutu da karatu. Daga nan sai muka kai su Makarantar Makafi ta Abuja,” inji shi
Da aka tambaye shi me ya sa ya ki yarda ’ya’yansa su yi bara? Sai ya ce “Ai bara ba abar alheri ba ce, saboda kashe zuciya take yi, kuma mutum ba zai yi kima ba a idon jama’a. Ni da kake ganina talaka ne amma duk da haka ’ya’yana ba su taba yin bara ba.”
Ya yi kira ga iyayen da ’ya’ya da suke da lalurar nakasa su sanya su a makarantar zamani don inganta rayuwarsu.
Shi kuwa Augustine wanda ke zaune a kauyen Igu da ke makwabtaka da kauyen Piko-Panda cewa ya yi ya taimaka wa Malam Adamu ne saboda Allah kawai. “Na taimaka masa ne saboda Allah, kuma ina so jama’a su gane cewa ba sai dan uwanka ko kabilarka ko wanda kuka hada addini daya za ka taimaka masa ba. Duk wanda zai yi taimako ya yi saboda Allah. Ka ga, ni Kirista ne shi kuma Malam Adamu Musulmi ne amma kuma na taimaka masa,” inji shi.
Da yake karin bayani kan lamarin, Sarkin garin Panda, Amadu Indagi cewa ya yi yana alfahari da matakin da Malam Adamu ya dauka na sanya ’ya’yansa makafi a makaranta. “Wannan abin alfahari ne. Mutanen garin Panda mun ji dadi da Malam Adamu ya sanya ’ya’yansa makafi a makaranta maimakon su yi bara. Saboda haka wannan abin koyi ne ga duk wani mai da da Allah Ya jarraba da lalurar nakasa,” inji shi.
Shugaban Makarantar Makafi ta Abuja, Misis Regina Dung ta ce ’ya’yan Malam Adamu suna da himma da kwazo a karatu.
Misis Regina ta ce akwai yara makafi da yawa da suke bukatar taimakon kayan karatu a makarantartar. Saboda haka sai ta yi kira ga masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kansu su kawo musu dauki wajen taimaka wa yaran da kayan karatu don inganta iliminsu.