Ba zan binciki Lamido ba – Badaru
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya nuna damuwa kan yadda ake sanya ido cewa zai binciki tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido, inda ya ce ba ya da burin bincikarsa amma ba zai hana Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) yin aikinta a jihar ba. Gwamna Badaru Abubakar ya […]
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya nuna damuwa kan yadda ake sanya ido cewa zai binciki tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido, inda ya ce ba ya da burin bincikarsa amma ba zai hana Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) yin aikinta a jihar ba.
Gwamna Badaru Abubakar ya fadi haka a ganawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar a ranar Juma’ar da ta gabata lokacin bikin cika kwana 100 a karagar mulkin jihar, inda ya ce jami’an Hukumar EFCC suna gudanar da aikinsu a jihar na zakulo badakalar da jami’an tsohuwar gwamnatin suka tafka.
Ya ce jami’an EFCC suna nan suna shiga ma’aikatun gwamnati don neman bayanan ayyukan gwamnatin da ta gabata domin samun madogarar da za su gudanar da ayyukansu. “Ba ni da burin tuhumar kowa duk da cewa Hukumar EFCC tana jihar nan tana aikinta. Ba zan shiga aikinsu ba zan ba su dama su yi aikinsu kamar yadda doka ta ba su domin aikinsu ne su gudanar da bincike su kama marar gaskiya su kuma hukunta shi komai girmansa saboda haka a bar su su yi aikinsu,” inji shi. Gwamna Badaru ya ce sun samu jihar a cikin talauci da kunci, inda gwamnatinsa ta iske Naira miliyan 16 kacal a asusunta, inda ya ce hatta asusun gwamnati na ko-ta-kwana ba ko sisi a ciki, kuma ga shi an bar su da dimbin bashin ayyukan kwangila har Naira biliyan 14 da kudin jarrabawar yara ta WAEC da NECO.
Ya ce kason kudin da jihar ke samu daga Asusun Tarayya ya yi kasa sosai amma duk da haka suna bakin kokarinsu wajen biyan albashin ma’aikata a kan lokaci, inda ya ce sun dauki matakan hana facaka da dukiyar gwamnati ta rage kudin da ake kashewa a ayyukan da ba su da muhimmanci ga jihar.