Ba zan ce ban tabuka komai ba-Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bisa la’akari da halin da gwamnatinsa ta samu kasar na “Rashin tanadi da rugujewar tattalin arziki” ba za a ce bai tabuka komai ba. Mai Magana da Yawun Shugaban kasar, Femi Adesina ya ruwaito Buhari yana bayyana haka a birnin Landan jiya yayin da ya karbi bakuncin kungiyar […]

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bisa la’akari da halin da gwamnatinsa ta samu kasar na “Rashin tanadi da rugujewar tattalin arziki” ba za a ce bai tabuka komai ba.
Mai Magana da Yawun Shugaban kasar, Femi Adesina ya ruwaito Buhari yana bayyana haka a birnin Landan jiya yayin da ya karbi bakuncin kungiyar ’yan Najeriya da ke zaune a kasashen waje karkashin jagorancin shugaban kungiyar Mista Charles Efe Sylvester.
Shugaba Buhari ya ce muggan mutane sun sace arzikin kasar kuma sun sanya ’yan kasar cikin matsanancin talauci.
Ya baiwa ’yan Najeriya tabbacin cewa zai yi duk abin da zai iya na rike amanar da ’yan kasar suka bashi kuma ba zai ci amanar da suka bashi ba.
“Ina farin ciki mutane kamar ku sun kasance zun zo nan da kansu don kare martabar kasarsu. Kun nuna karfin hali da sadaukar da kai. Ina mai tabbatar muku da cewa ba za mu ci manar da kuka ba mu ba kuma za mu yi kokari wajen rike amanarku”. Inji shi.