Ba zan ce uffan kan rikicin NNPP a Kano ba — Kwankwaso

Jagoran na NNPP ya ce ba shi da abin da zai ce game da rikicin.

Ba zan ce uffan kan rikicin NNPP a Kano ba — Kwankwaso

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP kuma jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ba zai yi magana kan rikicin cikin gida da ke faruwa a jam’iyyar a Jihar Kano.

Da ’yan jarida suka tambaye shi game da rikicin a gidansa da ke Miller road a Kano, a ranar Talata, Kwankwaso ya ce ba shi da abin cewa.

“Ba na son yin magana game da batun. Don Allah kada ku sanya ni cikin abin da ba na da alaƙa da shi. Shugaban jam’iyya ya riga ya yi magana, kuma yana ci gaba da magana a kai, ku tuntuɓe shi,” in ji shi.

Aminiya ta ruwaito yadda rikicin cikin gida ya sanya shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, ya dakatar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Baffa Bichi da Kwamishinan Sufuri, Muhammad Diggol.

Shugaban jam’iyyar, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya bayyana cewa an dakatar da su ne saboda zargin rashin girmamawa jam’iyyar.

Kazalika, ya ce sun yi amfani da muƙamansu ba bisa ƙa’ida ba, da rashin biyayya ga jam’iyyar.

Dakatarwar ta biyo bayan wani yunƙurin da Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi na sasanta sakataren gwamnatin da ‘yan mazaɓarsa da suka samu matsala.

Haka kuma, sakataren ya nesanta kansa daga wata ƙungiya da ke neman raba Gwamna Yusuf da Kwankwaso, wanda ta ke yi wa gwamnan taken “Abba, ka tsaya da ƙafarka.”

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos