…Ba zan ci amanarku ba – Buhari a Sakkwato

Taron yakin zaben Shugaba Muhammadu Buhari a Jihar Sakkwato ya tara dimbin jama’a idan wadansu ke ganin kusan ya fi na dukan jihohin da Shugaba Buhari ya ziyarta a baya. Magoya bayan Jam’iyyar APC da wadansu jiga-jigan jam’iyyar a kasa sun shaida wa Aminiya wannan kididigar. Wannan taro ne ya faranta ran Buhari har ya […]

…Ba zan ci amanarku ba – Buhari a Sakkwato

Taron yakin zaben Shugaba Muhammadu Buhari a Jihar Sakkwato ya tara dimbin jama’a idan wadansu ke ganin kusan ya fi na dukan jihohin da Shugaba Buhari ya ziyarta a baya.

Magoya bayan Jam’iyyar APC da wadansu jiga-jigan jam’iyyar a kasa sun shaida wa Aminiya wannan kididigar. Wannan taro ne ya faranta ran Buhari har ya fada wa magoya bayan cewa ‘ba zan ci amanarku ba’.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a filin wasa na Giginya da ke birnin Sakkwato a shekaranjiya Laraba, ya kara tabbatar wa mutanen jihar abu uku, “Ina shaida maku shugabanci amana ne, kuma ba za mu bari a ci amanarku mu kyale ba, duk wanda ya yi laifi za mu tabbatar an hukunta shi.

“A lokacin da na zo a shekarar 2015, ku shaidu ne na yi alkawarin inganta tsaro da bunkasa tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa. Na cika wannan alkawari, kuma ina kara tabbatar muku duk wanda aka samu da laifi a kasar nan za a hukunta shi,” inji shi.

Daraktan Kamfe dinsa Mista Rotimi Amaechi ya kara tabbatar da kudirin gwamnati na hada dukan kasar nan da layin dogo.

Jagoran APC a Sakkwato kuma Daraktan Kamfe na Arewa maso Yamma, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a kalamansa ya ce ba za su bari jam’iyyar adawa a jihar ta samu ko kujerar kansila ba.

 

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa