Ba zan ci mutuncin kowa ba – Buhari

dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari ya ce ba zai ci mutuncin abokan adawa ba idan aka zabe shi a matsayin Shugaban kasa a zaben 28 ga Maris mai zuwa. Janar Buhari ya bayyana haka ne a jiya Alhamis a wata takarda mai taken: “karfafa makomar dimokuradiyya a Afirka: Sauyin […]

Ba zan ci mutuncin kowa ba – Buhari
Ba zan ci mutuncin kowa ba – Buhari

dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari ya ce ba zai ci mutuncin abokan adawa ba idan aka zabe shi a matsayin Shugaban kasa a zaben 28 ga Maris mai zuwa.

Janar Buhari ya bayyana haka ne a jiya Alhamis a wata takarda mai taken: “karfafa makomar dimokuradiyya a Afirka: Sauyin Hannu a Mulkin Najeriya” wanda ya gabatar a cibiyar tsaro ta Chatham House da ke birnin Landan.
Ya ce zai bar hukumomin yaki da cin hanci da rashawa su yi aikinsu kamar yadda doka ta tanada, “Kuma zan karfafa cewa duk wani yaki da za a yi da cin hanci da rashawa kada ya ginu a kan huce haushi ko cin dunduniya da mutunci,” inji shi.
Janar Buhari ya kara da cewa: “Ina takarar shugabancin Najeriya ne don kai ta gaci ba domin jawo wahala ba.” Ya ce idan aka zabe shi gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali wajen dakile almubazzaranci da almundahana, inda ya ce, “Wajen yin haka idan aka zabe ni zan kasance a gaba wajen bayar da misalai da kaina.”
Janar Buhari ya ce ba zai nada mutanen da aka tabbatar mahandama ba ne a mukaman gwamnatinsa “Almundahana ba zai samu matsuguni ba, kuma ba zan nada mahandama kan mukamai a gwamnatina ba,” inji shi. Ya ce, hukumomin tara kudaden shiga kamar NNPC da Hukumar Kwastam za su samu littafi daya ne kawai. Kuma za a rika bayyana wa jama’a abin da suka samar tare da bincikarsu a kai-a kai.
Ya ce hukumomin gwamnati da aka kafa domin yaki da almundahana za su samu ’yanci da ikon hukunta masu laifi ba tare da tsoma bakin gwamnati ko sanya siyasa ba.
Game da matsalar tsaro kuwa Janar Buhari ya ce yadda gwamnati take tafiyar da matsalar Boko Haram ya sanya ana yi wa Najeriya da sojojinta dariya a kasashen waje. Ya ce a matsayinsa na tsohon Janar na soja ya samu kwarewa kan aikin soja a baya, inda ya kawo misali da yakin Bama da na Kongo da na Saliyo da na Laberiya da Darfur da sauran ayyukan tabbatar da zaman lafiya a sassan duniya. “Amma game da batun hare-hare sojojinmu ba su samun tallafin da ya kamata balle kayan aiki don kawo karshen matsalar. Gwamnati ta gaza wajen fuskantar matsalar lamarin da ya jawo a yanzu muna dogaro da makwabtanmu don su ceto mu. Don haka ina tabbatar muku idan aka zabe ni Shugaban kasar, to kada duniya ta tayar da hankalinta game da Najeriya kamar yadda take ciki yanzu; domin zan dawo da matsayinta na mai daidaita al’amura a Afirka ta Yamma, kuma ko taki daya na Najeriya ba zai koma hannun makiya saboda zan mayar da hankali wajen kula da sojojinmu da ke aiki da wadanda suka ajiye aiki.”
A karshe ya ce “A ranar 28 ga Maris, Najeriya za ta yanke hukunci. Kodai ta zabi ci gaba da gazawa, ko kuma ta zabi canji na ci gaba. Na yi Imani jama’a za su yi zabin da ya dace.”