Ba zan daina sukar gwamnatin Tinubu ba — Farfesa Yusuf

Farfesa Yusuf gwamnatin Tinubu na son murƙushe duk mutumin da ke sukarta.

Ba zan daina sukar gwamnatin Tinubu ba — Farfesa Yusuf

Tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya zargi Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ƙoƙarin hana shi magana sakamakon sukar manufofinta da yake yi.

Yusuf, wanda ya yi ƙaurin suna wajen sukar gwamnati, Hukumar EFCC ta kama shi tare da gurfanar da shi a kotu bisa zargin rashawa.

Sai dai ya musanta dukkanin zarge-zargen, inda ya ce an shirya masa tuggu ne saboda dalilan siyasa.

Da yake magana yayin da yake tsare a gidan gyaran hali na Kuje, ya ce, “Wannan wani yunƙuri ne na hana ni yin magana kawai. Zarge-zargen EFCC ba su da tushe balle makama, kuma suna amfani da tsoffin maganganu marasa tushe.

“Ina da ƙwarin gwiwa cewa lauyoyina za su kare ni.”

Farfesa Yusuf ya kuma zargi jami’an tsaro da bibiyarsa da iyalansa.

“Tun tsawon watanni suke bin diddigin rayuwata, a zahiri da kafafen sada zumunta.

“Wannan gwamnati na amfani da hanyoyin danniya domin hana jama’a faɗin albarkacin bakinsu, kamar yadda aka saba a zamanin mulkin soja,” in ji shi.

Kama shi ya jawo ce-ce-ku-ce daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da kuma ’yan adawa, waɗanda suka bayyana hakan a matsayin yunƙurin muƙushe ’yancin faɗin albarkacin baki.

Wasu masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam, sun buƙaci a saki Yusuf nan take, inda suka ce suka da adawa ga manufofin gwamnati bai kamata a ɗauke su a matsayin laifi ba.

“Dimokuraɗiyya na buƙatar ra’ayoyi mabambanta. Amfani da tsoratarwa da shari’a don hana masu suka magana babbar barazana ce ga ’yancin jama’a,” in ji wani mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam.

Duk da kasancewarsa a tsare, Yusuf ya yi alƙawarin ci gaba da magana kan yadda gwamnatin Tinubu ta gaza.

Ya buƙaci ’yan Najeriya da su zama masu lura da kuma neman haƙƙinsu a wajen gwamnati.

“Wannan ba batuna ne ni kaɗai ba. Batun kare ’yancin jama’a ne da hana kowace gwamnati amfani da tsoro don muƙushe al’umma.

“Dole mu tashi tsaye don kare haƙƙoƙinmu,” in ji shi.

Yanzu haka dai yana tsare yayin da kotu ta ɗage zaman sauraron buƙatar bayar da belinsa zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu.