Ba zan daina takara ba matuƙar ina raye — Atiku
Atiku ya ce duk wanda jam’iyyarsa ta tsayar a 2027 zai mara masa baya.
Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar PDP a Zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya ce zai ci gaba da neman kujerar shugabancin ƙasar nan, matuƙar yana raye kuma cikin ƙoshin lafiya.
Atiku ya yi tsokaci kan lokutan da ya yi takara ba tare da samun nasara ba, yana mai cewa tsohon Shugaban Amurka, Abraham Lincoln sai da ya yi takara sau bakwai kafin ya kai ga nasara.
- Sarkin Kano: Sanusi II na shirye-shiryen komawa kujerarsa
- An Tsige Duk Sarakunan Jihar Kano —Majalisa
Atiku ya bayyana haka ne yayin wata hira da Sashen Hausa na Muryar Amurka.
“Tabbas, zan ci gaba da tsayawa takara matuƙar ina da rai da kuma ƙoshin lafiya,” in ji Atiku.
“Ko tsohon shugaban Amurka, Abraham Lincoln sai da ya yi takara sau bakwai kafin daga bisani ya yi nasara.”
Atiku mai shekara 77 a duniya, wanda zai cika shekara 81 a lokacin Babban Zaɓen 2027, ya yi martani game da rikicin da ke faruwa a jam’iyyar PDP, inda ya tabbatar da cewa dole ne ’ya’yanta su haɗa kai domin samun nasara a gaba.
“Duk da haka, idan aka yi la’akari da halin da jam’iyyar PDP ke ciki a yanzu, a bayyane yake cewa ɓangare ɗaya ba zai kai mu ga cin zaɓe ba. Akwai buƙatar goyon baya daga wasu jam’iyyun,” in ji shi.
A makon da ya gabata ne, Atiku ya ce yana tattaunawa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a Zaɓen 2023, Peter Obi, kan yiwuwar haɗewa waje ɗaya.
“Ga duk wanda yake tunanin za a samu rashin fahimta tsakanina da Obi, ina tabbatar muku da cewa babu abin da zai faru a tsakaninmu,” in ji Atiku.
“Kazalika, za mu mara wa duk wanda aka zaɓa ya wakilce mu a zaɓe mai zuwa.
“Na bayyana ƙarara a jawaban da na yi a baya cewa idan jam’iyyunmu za su haɗe su amince da ɗan takara daga yankin Kudu maso Gabas, matuƙar ya cancanta, za mu mara masa baya.
Atiku ya ce ya nemi shugabancin Najeriya har sau shida da suka haɗa shekarar 1993, 2007, 2011, 2015, 2019 da kuma 2023.
Ya yi takara a zaɓen fidda gwani a jam’iyyar SDP a 1993, amma ya sha kaye a hannun, Moshood Abiola.
Ya yi takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AC a zaɓen 2007, inda ya ƙare a mataki na uku a bayan Umaru Yar’Adua na PDP da Muhammadu Buhari na jam’iyyar ANPP.
Ya sake neman takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2011, inda ya sha kaye a hannun Goodluck Jonathan.
A 2014, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2015, inda ya sha kaye a zaɓen fidda gwani a hannun Muhammadu Buhari.
A shekarar 2017, ya koma jam’iyyar PDP, kuma ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar a Zaɓen 2019, inda ya sake shan kaye a hannun Muhammadu Buhari.
Takarar ƙarshe da Atiku ya yi ita ce ta 2023, inda ya sha kaye a hannun Shugaban Kasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu.