Ba zan gudu daga Najeriya zuwa wata kasa ba – Ministar Mai
Ministar Albarkatun Man fetur Misis Diezani Alison-Madueke, ta ce ba ta da niyyar ficewa daga kasar nan zuwa wata kasar waje duk da zargin da ake yi mata na tafka almundahanar biliyoyin Dala. Misis Diezani Alison-Madueke tana mayar da martani ne ga labarin da ake bazawa a shafukan intanet cewa ta nemi mafakar siyasa a […]
Ministar Albarkatun Man fetur Misis Diezani Alison-Madueke, ta ce ba ta da niyyar ficewa daga kasar nan zuwa wata kasar waje duk da zargin da ake yi mata na tafka almundahanar biliyoyin Dala.
Misis Diezani Alison-Madueke tana mayar da martani ne ga labarin da ake bazawa a shafukan intanet cewa ta nemi mafakar siyasa a kasashe shida bayan kayen da Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar ta sha a zaben 28 ga Maris din da ya gabata.
Diezane wadda ke magana da manema labarai na fadar Shugaban kasa a shekaranjiya Laraba, ta ce, “Bari in fadi karara, Najeriya kasata ce, kuma babu inda zan je.
Ministar ta ci gaba da cewa: “Ba wani laifin da na aikata da zan gudu ko in nemi mafaka a wata kasa, ba gaskiya ba ne zargin da ake yi min na kashe kudaden da ake cewa na kashe kimanin Naira biliyan goma wajen yawo a jirgin sama.”
Minista Madueke ta ce ya kamata a daina musu irin wannan kazafi ta shafukan intanet, inda ta ce wasu matsorata ne ke yi, domin a cewarta ta yi wa Najeriya aiki iyakar iyawarta a Ma’aikatar Man fetur din.
Ministar ta kuma musanta rade-radin da ake yi cewa ta je gidan tsohon Shugaban kasa Janar Abdussalami Abubakar domin rokonsa ya nema mata sassauci a wurin Shugaban kasa mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari.
Ta ce, tuni Kamfanin Mai na kasa (NNPC) ya fara maido da wani bangare na Dala biliyan daya da miliyan 480 (kimanin Naira biliyal 280) ga Asusun Tarayya da aka yi zargin ya ki mikawa ga asusun.