Ba zan iya aikin albashin Naira dubu 200 in bar kasuwanci ba – Warshu
Malam Muhammadu Warshu dan kasuwa ne da ke hada-hadar albasa daga Arewa zuwa Kudu, a zantawar sa da Aminiya ya fadi-tashin da ya yi har ya kafu a harkar, kuma ya yi tsokaci kan alfanun kasuwancin albasa da kalubalen da ke tattare da ita: Mene ne takaitaccen tarihinka? Sunana Alhaji Muhammadu Warshu Matankari, an haife […]
Malam Muhammadu Warshu dan kasuwa ne da ke hada-hadar albasa daga Arewa zuwa Kudu, a zantawar sa da Aminiya ya fadi-tashin da ya yi har ya kafu a harkar, kuma ya yi tsokaci kan alfanun kasuwancin albasa da kalubalen da ke tattare da ita:
Mene ne takaitaccen tarihinka?
Sunana Alhaji Muhammadu Warshu Matankari, an haife ni a garin Matankari da ke Karamar Hukumar Karaye a Jihar Kano a 1983. Na yi firamare a Matankari bayan na kammala aka kai ni karatun allo a Unguwar Kabuga a birnin Kano dalilin haka ban samu tafiya sakandare kai-tsaye ba. Bayan na samu abin da na samu na karatun allo na yi sana’o’i da dama a lokacin a Unguwar Kabuga da ke Karamar Hukumar Gwale.
Yaya ka samu kanka a Legas?
Na taho Legas a shekarar 2003 ta dalilin kanen mahaifina marigayi Alhaji Umaru Agege wanda yake kasuwancin albasa a Legas kuma ya kasance mutum ne mai jajircewa da himma domin a lokacin da yake raye ba ya da kasala ko kadan wajen harkokin kasuwancinsa domin a wancan lokaci a duk mako sai ya je Jihar Sakkwato daga Legas ya sayo albasa ya komo Legas a wannan mako bayan ya sayar ya kuma komawa. Haka yake yi duk mako, kana mutum ne mai taimakon jama’a, burinsa a koyaushe ya ga ya kafa al’umma a irin haka ne ni ma ya dauko ni ya koya min kasuwancin tun daga tushe. Domin a lokacin na zo na iske shi yana da rumfuna da dama a Kasuwar Ilepo a Legas, amma duk da haka bai bar ni a rumfar kasuwa ba, domin kada ya sangarta ni sai ya nuna min hanyar da zan koyi kasuwanci daga tushe inda na fara da taimaka wa masu harkar suna sallama ta har na kai matakin da ake ba ni albasar ina shiga kasuwa in kasa wato na yi kashi tun ina kasa irin ruba-ruba da ake kiranta Waiwai ina sayar da kashi Naira 5 ko Naira 10, har na kai ga zan kasa mai kyau in sayar. Bayan da na samu natsuwa na koma Arewa na ci gaba da karatun sakandare inda in an yi hutu nake komowa Legas in ci gaba da kasuwanci har na kammala karatun sakandare kuma zuwa yanzu ina karatu a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) da ke Kano ina karatun lokaci-lokaci (part time), kuma ina ci gaba da kasuwancina.
Wannan bappa nawa da ya yi sanadiyyar zuwata Legas, Allah Ya yi masa rasuwa a bara ina fata Allah Ya jikansa, ina kuma fatar in yi koyi da shi yadda ya kafa mutane a kasuwar nan suke samun rufin asiri ni ma in kafa wadanda ko bayan bana nan za su rika tunawa da ni suna yi min addu’a. Wani abu da na koya daga gare shi, shi ne idan kana kasuwanci kana da yara da ke taya ka aiki to ka kyautata musu ka yi masu ihsani, sannan abokan kasuwancinka ka yi musu adalci idan ka sayo kaya da sauki, to, su sani wato su ma ka saukaka musu, idan kaya ya yi tsada sai ka yi musu bayani su ma su sanar da abokan kasuwancinsu, domin adalci a kasuwa shi ke sa mutum ya samu ci gaba kasuwancinsa ya yi albarka
Me za ka iya cewa a kan kasuwancin albasa?
Kasuwancin albasa harka ce mai tarin rufin asiri, kusan zan iya cewa a duk kasuwar gwari babu hajar da ake sayarwa wacce ta kai albasa rufin asiri. Domin akasarin kayan gwari suna da lokaci, idan lokacinsu ya wuce za ka ga masu sayar da irin wadannan kayayyaki suna komowa su yi harkar albasa ce, amma mu da muka riki albasa a matsayin harkarmu ta dindindin babu lokacin da take yanke mana a ce mun mu bar ta mun koma wata harkar ta daban. Ka ga masu sayar da doya da tumatir da wake da dankali dukkansu in kayansu ya ja baya suna zuwa su rabi wannan harka tamu ta albasa, ka ga wannan kadan ne daga cikin rufin asirin albasa. Mafi tsadarta ba ta wuce buhu Naira dubu 45 zuwa 50 wanda a baya ta yi tsadar da ta kai buhu Naira dubu 60, kana mafi araharta buhun ta ba ya wuce Naira dubu 10 sai dai a da can takan yi arahar da ake sayar da buhu Naira dubu uku zuwa dubu uku da 500.
A ina ne kuke sayo albasar daga Arewa ?
Akasari muna sayo albasa ce daga Jihar Sakkwato nan ne albasa ba ta yankewa a kowane lokaci. Kana abokan cinikinmu da akasari Yarbawa ne albasa ’yar Sakkwato suka fi amfani da ita, sannan akwai wacce muke sayowa a Kano wacce ake kiranta ’yar Zariya wato jar albasa irin wannan abokan kasuwancinmu Ibo suke amfani da ita. Muna zuwa duk Arewa duk mako mu sayo kaya da kudinmu sai dai muna bai wa abokan cinikinmu bashi ne idan sun ba mu kudin wancan mako sai mu ba su wani kayan. In mun shiga sabon mako su ba mu kudi su karbi wani kayan a haka muke kasuwanci da abokan cinikinmu. Mu kudinmu muke sawa mu sayo amma sai mu zo mu raba bashi wannan shi ne babban kalubalen harkar tamu, wato bashi amma cikin ikon Allah a haka ake yin harkar kuma a samu rufin asiri. Yanzu haka mukan sauke kaya sau biyu a mako, riba kuma ya danganta da yanayin kayan da lokaci, akasari an fi samun riba a lokacin da kayan ke tsada ko idan ya yi wuya domin a nan Kurmi idan kaya ba ya da daraja to mu ’yan kasuwar ma ba ma yin daraja, kuma babu dan kasuwar da ke samun alfanu idan ba a kallonsa da daraja. Don haka mun fi samun alfanu a lokacin da albasa ke tsada wato lokacin da take da daraja.
Zuwa yanzu wane alfanu ka samu a harkar albasa?
Na samu alfanu da dama, na farko shi ne jama’a wato Allah Ya ba ni jama’a a wannan harka tawa sannan kuma na samu jari wanda mutane da dama ke amfana da shi, domin alfanun kasuwanci irin na fatauci yana da dama sosai don in mutum daya ya fid da kudi kamar Naira miliyan biyar ya je Arewa ya sayo kaya ya kawo nan Kudu, to in Allah Ya yarda akalla mutum 300 za su amfana da wannan dukiya ka ga a nan an samar wa jama’a da dama abin dogaro ke nan. Tun daga kan manomi in ya sayar ya samu karin kwarin gwiwar da zai koma ya sake nomawa, haka dillalai da ’yan dako da direbobi da masu sauke kaya da ’yan kasuwar da za su yi sari da masu sayen daidai. Haka abin yake har zuwa lokacin da kayan zai kare don haka nake shawartar masu kudi a hannu su fito su juya su yi kasuwanci yadda za su karu, al’umma ma ta karu baki daya. Amma ba daidai ba ne mutum ya makare kudi a banki ko a gida yana kallonsu, idan ka fito da su ka yi kasuwanci sai ka karu, al’umma ta karu, arziki ya yalwata a kasa.
Haka zalika a wannan harka na yi aure na hayayyafa kuma nake kula da iyalina, da ’ya’yan ’yan uwa da nake daukar dawainiyar karatunsu. Kuma yanzu haka na kafa yara da dama da ke karkashina suna wannan harka wadannan kadan ne daga cikin alfanun kasuwancin albasa. Kuma a yanzu ba zan iya aikin albashi ba, ko da kuwa za a ba ni Naira dubu 200 ne a wata, domin na saba da kasuwanci ba zan iya jira sai karshen wata wani ya ba ni albashi ba. Na fi gane wa kasuwanci na yau in na samu ko gobe ban samu ba na san jibi Allah zai kawo, wannan ya fiye min in jira sai karshen wata sannan a ba ni.
Kana da kira ga gwamnati?
Kirana ga gwamnati ta tallafa wa manoma yadda ya dace, domin idan gwamnati ta karfafi manoma suka yi noma, to an rage matsaloli fiye da kashi 50 cikin 100. Don mu a Arewa babu abin da za a yi a taimaki al’umma fiye da taimaka wa noma, a yi musu taimakon da zai rike su, su samu taki da sauki a kan lokaci ba irin taimakon da za a bayar amma ya tsaya kan manoman littafi ba, su kuma manoma na zahiri ya ki riskarsu. Idan an taimaki manoma yadda ya kamata za a samu yalwar arziki fiye da yadda ba a zato.