Ba zan iya jira sai wani ya ba ni ba -Makaho MikoYaro
Wani makaho mai suna Malam Minka’il Mai Tukunya, wanda aka fi sani da MikoYaro Makadi Wudil, ya ce duk da lalular rashin ganin da yake fama da ita babu dalilin da zai sa shi ya yi bara saboda yadda sana’ar sayar da maganin bera da kwari take rufa masa asiri.dattijon, dan asalin Jihar Kano, yana […]
Wani makaho mai suna Malam Minka’il Mai Tukunya, wanda aka fi sani da MikoYaro Makadi Wudil, ya ce duk da lalular rashin ganin da yake fama da ita babu dalilin da zai sa shi ya yi bara saboda yadda sana’ar sayar da maganin bera da kwari take rufa masa asiri.
dattijon, dan asalin Jihar Kano, yana gudanar da kasuwancinsa ne a Kasuwar Barci da ke Tudun Wada, Kaduna. A zantawarsa da Aminiya, ya ce albarkacin sana’arsa, wadda ya shafe shekara 17 yana gudanarwa ya samu wadatuwa ta ci da sha da tufafi da taimaka wa ’yan uwa da abokan arziki. Sannan kuma ya bayyana cewa matansa uku da kuma ’ya’yansa biyar su ma sun dogara ne da wannan sana’ar.
Ya ci gaba da cewa: “Ina aikawa Kano ne don a sayo min kayayyakin. Sannan kullum da safe nakan sa dana Muhammad Sagir da ya shirya min kayan ta inda masu bukata na zuwa zan iya mika hannuna don lalubo musu abin da suke bukata. Wajen karbar kudi kuma nakan ajiye kananan kudi a aljihu daban, hakazalika manyan na ware su guri daban. Saboda idan mai saye ya tambayi canji, sai na wai wa yi aljihun da ya dace don sallamarsa.” Injishi
Malam Minka’ila ya kara da cewa:“Yau shekarata 72 a duniya, na yi sana’ar sayar da tukwane da sauran sana’o’i daban-daban kafin na rasa idanuna a shekarar 1999 sanadiyyar ciwon yanar ido (Glaucoma). duk da wannan ni ba zan fasa nema ba, saboda abin da na ki jini a rayuwata shi ne na a ce yau mutum ya kwanta yana jira sai wani ya ba shi. Ya dace masu lalura irin tawa da kuma sauran jama’a, musamman ma matasa, su mike saboda ta haka ne kawai za su iya magance mutuwar zuci.”