Ba zan iya komawa aiki ba – Suntai 1

Wani faifan bidiyo da aka sanya a shafin Youtube na Internet ya nuno Gwamnan Jihar Taraba, Mista danbaba Suntai yana cewa, ba zai iya komawa bakin  aiki a matsayinsa na Gwamna ba.Gwamna Suntai wanda ya hadu da hadarin jirgin sama a shekarar 2012, yana fama da doguwar jinya da ta kai shi kasashen Jamus da […]

Ba zan iya komawa aiki ba – Suntai 1

Wani faifan bidiyo da aka sanya a shafin Youtube na Internet ya nuno Gwamnan Jihar Taraba, Mista danbaba Suntai yana cewa, ba zai iya komawa bakin  aiki a matsayinsa na Gwamna ba.
Gwamna Suntai wanda ya hadu da hadarin jirgin sama a shekarar 2012, yana fama da doguwar jinya da ta kai shi kasashen Jamus da Amurka, kafin wasu mukarrabansa su dawo da shi kasar nan a bara.
Batun ko Gwamna Suntai yana da koshin lafiyar da zai iya komawa kan mulki ne ya tukuikuye siyasar Jihar Taraba, inda ko a’yan kwanakin nan an baza labarin cewa wasu mukarrabansa na ta kokarin mayar da shi kan karagar mulki, har ma suka yi yunkurin kai shi wurin Shugaba Goodluck Jonathan don ya taimaka.
Hoton bidiyon wata kungiyar yaki da cin hanci da rashawa da ke Legas ta nuna wa manema labarai a karshen makon jiya, inda Suntai ya nuna fatar samun lafiya amma ya ce zai dauki lokaci mai tsawo.
Lokacin da Aminiya ta tuntubi kakakin Suntai Sylbanus Giwa ya ce bai kalli bidiyon ba, kuma ba ya da masaniyar Gwamna Suntai ya yi irin wannan hirar.
Bidiyon ya nuna Suntai yana amsa tambayoyi daga wani da ba a bayyana sunansa ba.
Da aka tambaye shi yaushe zai dawo kujerarsa ta Gwamna? Sai Suntai ya ce “Ba zan iya fada ba amma ya kamata a ce na koma ofis saboda ina son ku ba ni goyon baya. Amma ka san gaskiya ba ni da koshin lafiyar da zan koma ofis a yanzu.”
Da aka tambaye shi wane lokaci yake ganin zai samu koshin lafiyar da zai koma aiki, sai Suntai ya ce: “Na san nan da wani lokaci zan samiu koshin lafiyar da zan gudanar da aikina. Amma zai dauki lokaci.”
A sakonsa ga al’ummar Jihar Taraba, Suntai ya ce “Ya kamata mu koyi yadda za mu rika bin hanyar mahalicci. Yin haka zai sa mu samu ingantacciyar rayuwa. Amma idan muka kauce hanyar Ubanagiji sai mu yi ta jidali, wannan shi ne abin da yake faruwa da ni. Tuni na fara kirga sauran kwanakin da suka rage mini a duniya saboda lamarin shaye-shaye, shaye-shaye. Shaye-shaye ba abu ne mai kyau ba.”
Da ya waiwayi ’yan Najeriya sai ya bukaci su ce koma ga Allah, su ajiye abubuwan da Ya hana “Abin takaici shi ne mun zabi mu ci gaba da aikata wasu abubuwa duk da cewa mun san Allah ba Ya so, abin takaici ina cikin wadanda suke aikata irin wadannan abubuwa.”