Ba zan ja layi kan sace kudin al’ummar Kaduna ba – El-Rufa’i

Sabon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya ce gwamnatinsa ba za ta ja layi don kyale wadanda suka saci kudin jama’ar jihar ba. Gwamna Nasiru El-Rufa’i ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata, inda ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar an bi hanyar da ta kamata wajen kwatowa ko karbo kudin […]

Ba zan ja layi kan sace kudin al’ummar Kaduna ba – El-Rufa’i
Ba zan ja layi kan sace kudin al’ummar Kaduna ba – El-Rufa’i

Sabon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya ce gwamnatinsa ba za ta ja layi don kyale wadanda suka saci kudin jama’ar jihar ba.

Gwamna Nasiru El-Rufa’i ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata, inda ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar an bi hanyar da ta kamata wajen kwatowa ko karbo kudin da aka sace a jihar daga hannun wadanda suka sace su.
Gwamna El-Rufa’i ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan ya karbi rahoton kwamitin karbar mulki na Jam’iyyar APC a jihar.
Ya kara da cewa gwamnatin PDP ta kasa ciyar da jihar gaba a cikin shekarun da ta yi tana mulkin jihar.
“Ba za mu yarda da abin da aka yi ba, dole ne a bayyana gaskiyar yadda al’amura suka faru musamman wajen bayyana yadda aka kashe kowane sisin kwabo a jihar. Kuma duk wanda aka samu da daukar wadannan kudade za mu bi shi cikin lallabi ya maido su, idan kuma ya ki za mu dauki matakin ba sani ba sabo,” inji shi.
Ya kara da cewa: “Wannan abu ne da muka shirya yi, domin wannan jihar ta sha wahalar rashin ci gaba saboda ba a kashe kudi ta hanyoyin da suka kamata. Saboda haka ba zan ja layi ba, in ce abin da ya wuce ya wuce, domin barnar baya na iya shafar gaba.”
Gwamna El-Rufa’i ya gargadi ’yan siyasa cewa su sani duk wanda ya ki tsayawa ya yi wa jama’a aiki, mutane a shirye suke su ki zabarsa bayan shekara hudu.
“Wannan abu ne mai muhimmanci kuma sakon da nake fada wa abokan aikina ke nan cewa yanzu mun gane cewa dole ne mu yi wa jama’a aiki ko su ki zabarmu bayan shekara hudu kuma babu wata mafita da ta wuce mu yi wa jama’a aiki. A nan Jihar Kaduna ni da mataimakina za mu yi aiki yadda ya kamata, domin kawo ci gaba mai inganci ga jihar da rayuwar al’ummarta. Idan muka kasa, jama’a sai su ki zabarmu kuma su zabi wasu nan gaba, saboda haka wannan abu ne mai kyau kuma haka ya kamata ya zama,” inji shi.
Gwamna El-Rufa’i ya kuma shaida wa wadanda za su yi aiki da shi cewa su shirya sadaukar da albashinsu da alawus dinsu domin yi wa jama’ar jihar aiki. Ya ce dole gwamnatinsa ta rage yawan albashi da alawus din wadanda za ta bai wa mukamai domin a samu damar yi wa jama’ar jihar aiki a inganta rayuwansu.