Ba zan janye wa Atiku takara ba don ni ne gaba da shi – Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ce ba zai taba janye wa tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar a takarar shugabancin kasa da yake yi a Jam’iyyar PDP ba. A ranar Talata ce bayan wani taro da Atiku ya yi da jiga-jigan PDP a Jigawa, ya bayyana cewa ya yi amanna cewa Sule […]

Ba zan janye wa Atiku takara ba don ni ne gaba da shi – Sule Lamido
Ba zan janye wa Atiku takara ba don ni ne gaba da shi – Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ce ba zai taba janye wa tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar a takarar shugabancin kasa da yake yi a Jam’iyyar PDP ba.

A ranar Talata ce bayan wani taro da Atiku ya yi da jiga-jigan PDP a Jigawa, ya bayyana cewa ya yi amanna cewa Sule Lamido zai iya janye masa takara a matsayinsa na yayansa. Ya ce kasancewar Lamido kane ne gare shi, ya yi imanin cewa zai iya janye masa, tunda dukansu biyun akidar siyasarsu daya ce.

Atiku ya shaida wa mahalarta taro a Dutse, cewa mahaifiyarsa ’yar asalin kauyen Jigawar Sarki ne da ke karamar Hukumar Dutse, kafin iyayenta su yi hijira zuwa Jihar Adamawa, inda a can ne ta haife shi.

Sai dai da yake mai da martani ga Atiku, ta wata sanarwa da Kakakinsa Adamu Usman ya fitar, Alhaji Sule Lamido, ya ce ba zai taba janye wa Atiku ba. 

“Tabbas Atiku ya girme ni, amma idan ana maganar siyasa, ai ni yayansa ne, shi yaro ne. Saboda a lokacin da nake Majalisar Wakilai a 1979, Atiku bai yi ritaya daga aikin Kwastam ba.

“Idan kuma Atiku ya ce za a bi ta yawan shekaru ne a zabi dan takara, to shi ya janye ya kyale wa Buhari mana, tunda shi ma Buhari ya fi shi yawan shekaru,” inji Lamido.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Lamido ya nuna juriya da hakuri da biyayya da kuma tsayawa ka-in-da-na’in a kan raya Jam’iyyar PDP da inganta tafarkin dimokuradiyya, duk kuwa da irin bibiyar da ake nuna masa. Lamido fa da shi aka kafa PDP, kuma har yau bai taba ficewa daga cikinta ba. Don haka Lamido ne ya fi cancantar a janye masa takarar, saboda ya fi sauran karsashi da kyakkyawar manufa da kwarewa da sanin makamar siyasa da kuma karfin iya kokawa da APC.” 

 

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa