Ba zan koma APC ba- Babangida Aliyu

Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dokta Babangida Aliyu ya ce bai da niyyar komawa Jam’iyyar APC daga Jam’iyyar PDP. Babangida Aliyu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi jim kadan bayan wasu ‘yan siyasa sun canja sheka daga wasu jam’iyyu zuwa APC ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Neja, Alhaji […]

Ba zan koma APC ba- Babangida Aliyu

Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dokta Babangida Aliyu ya ce bai da niyyar komawa Jam’iyyar APC daga Jam’iyyar PDP.

Babangida Aliyu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi jim kadan bayan wasu ‘yan siyasa sun canja sheka daga wasu jam’iyyu zuwa APC ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Neja, Alhaji Aminu Yusuf.

“Bani da niyyar komawa APC saboda na yarda da Jam’iyyar PDP. Na samu damar komawa APC a lokacin da na jagori gwamnoni 7, amma sai na ki barin jam’iyyar saboda na yarda da ita.

 

“A lokacin abin da muke bukata shi ne a gyara wasu abubuwa, ba wai mu bar jam’iyyar ba. Da ace ina da son raid a na koma APC a lokacin. Da yanzu watakila na zama minsita.”