Ba zan nemi afuwar kowa ba – Gwamna Nyako

Gwamna Murtala Nyako na Jihar Adamawa ya ce ba zai nemi afuwar kowa ba game da wasikar da ya rubuta wa kungiyar Gwamnonin Arewa inda ya zargin Gwamnatin Jonathan da neman karar da mutanen Arewa, “Ban ga dalilin baiwa wani hakuri ba”, inji shi.Gwamnan yana mayar da martani ne ga masu cewa ya nemi afuwa […]

Ba zan nemi afuwar kowa ba – Gwamna Nyako
Ba zan nemi afuwar kowa ba – Gwamna Nyako

Gwamna Murtala Nyako na Jihar Adamawa ya ce ba zai nemi afuwar kowa ba game da wasikar da ya rubuta wa kungiyar Gwamnonin Arewa inda ya zargin Gwamnatin Jonathan da neman karar da mutanen Arewa, “Ban ga dalilin baiwa wani hakuri ba”, inji shi.
Gwamnan yana mayar da martani ne ga masu cewa ya nemi afuwa a fadar Shugaban kasa, inda ya ce lallai ba karya ya rubuta ba, abin da ke faruwa ya rubuta. Ya ce ai sau biyu ya rubuta wa Shugaba Goodluck wasika, amma ko ci-kanka bai ce masa ba don haka, ba zai nemi afuwar kowa ba.
Gwamna Nyako ya bayyana mamakinsa da ake yada cewa taron tsaro da suka yi da Shugaba Jonathan ya yi Allah wadai da wasikar da ya rubuta. Ya ce sam ba a yi haka ba, inda ya ce ya rubuta wasikar ce da kyakkyawar manufa domin ankarar da shugabanni game da irin abubuwan da ke faruwa.
Ya ce, “A kan me za a soke ni? Abin da ya fi dace musu shi ne su kama bakinsu su yi shiru, domin kuwa ba yadda zan yi wannan maganar don babatu don haka a bar maganar”.
Ya ce amfani da karfin soja a tarihin duniya bai taba kawo gyara da zaman lafiya a cikin al’umma ba. Kuma ya ce hakan ne ya sa ya aika wa Shugaban kasa tare da gwamnonin Arewa wasika har sau biyu kuma babu amsa.
Ya ci gaba da cewa kamar yadda aka sani aikin sojoji a kasarmu shi ne su tsare kasa game da shigowar abokan gaba. Amma ba su ci gaba da tsaro a cikin kasa, kamar yadda suke yi a yanzu ba.
Ya ce an koyar da soja dabaru daban-daban na yaki domin ba su nasara a kan abokan gabansu, amma kawo soja don su yi tsaro ko dawo da zaman lafiya a cikin kasa ba zai haifar da abin kirki ba.
Gwamna Nyako ya ce abin da ke faruwa yanzu shi ne, sojoji na cin zarafin al’ummar da ba su san hawa ko sauka ba a jihohin ukun. Ya ce yana nan a kan ra’ayinsa game da wasikar da ya rubuta.
Gwamnan ya ce ya kamata gwamnonin Arewa su san cewa lokaci ya yi da za su kalli matsalar tsaro da fuskar da ta dace domin kawo karshen kashe jama’a da sojoji ke yi ba gaira ba dalili. Kuma su maida hankali kan kalubalen da ke damun jama’ar yankin Arewacin Najeriya.
Ya ce dalilinsa na rashin halartar taron Gwamnonin Arewa shi ne sakamakon rashin magana a kan matsalolin tsaro da kuma talauci da suka shafi Arewa. “Kullum in an zauna maganar ba ta wuce ta Gidauniyar Sardauna ba,” inji shi.
Ya ce Arewa na fama da matsaloli da dama, inda ya ce ya kamata taron ya dauki matakin tattaunawa don don magance wadannan matsalolin da suka shafi yankin baki daya. Amma gwamnonin suka ce abin tattaunawa ita ce matsalar manoma da makiyaya kawai.
Ya ce dalilinsa na biyu kuma shi ne, ba a karo na daya ko na biyu ba aka gudanar da taron amma ba abin da kungiyar ta taba tsinanawa. Kamata ya yi a bayyanar da irin taron nan a taron jama’a aji irin nasu ra’ayin. Ya ce bisa ga dukkan alamu gwamnonin ba su da shiri kan kawo karshen matsalar tsaro a yankin.
Gwamnatin Tarayya dai ta rage jami’an tsaron lafiyar Gwamnan daga 120 zuwa 30. Kuma rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da hakan, sai dai kawo yanzu babu bayani daga hukumomin da abin da ya shafa kan dalilin daukar matakin.