Ba zan rushe shugabannin kananan hukumomi ba – Gwamna Badaru

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya ce ba zai rushe zababbun shugabannin kananan hukumomin jihar da aka zaba lokacin tsohuwar gwamnatin Sule Lamido ba, har sai sun cika wa’adin mulkinsu.A wata ganawa da Gwamna Badaru ya yi da shugabannin kananan hukumomin jihar 27 da ake baza jita-jitar za su koma Jam’iyyar APC su […]

Ba zan rushe shugabannin kananan hukumomi ba – Gwamna Badaru
Ba zan rushe shugabannin kananan hukumomi ba – Gwamna Badaru

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya ce ba zai rushe zababbun shugabannin kananan hukumomin jihar da aka zaba lokacin tsohuwar gwamnatin Sule Lamido ba, har sai sun cika wa’adin mulkinsu.
A wata ganawa da Gwamna Badaru ya yi da shugabannin kananan hukumomin jihar 27 da ake baza jita-jitar za su koma Jam’iyyar APC su da ’yan Majalisar Jihar da na tarayya a gidan gwamnati ne Gwamnan ya bayar da wannan tabbaci kamar yadda wani dan Majalisar Tarayya ya shaida wa wakilimmu bayan ya bukaci a sakaye sunansa.
dan majalisar ya ce a ganawar da Gwamnan ya yi da shugabannin kananan hukumomin da su ’yan majalisar a kan shugabannin kananan hukumomin Gwamnan ya ce ba zai rushe shugabannin daga mukamansu ba sai wa’adinsu ya cika.
dan majalisa ya ce amma kananan hukumomi biyu da Gwamna Lamido ya nada musu kantomomin riko, gwamnatin jihar za ta sauke su ta gudanar da sabon zabe, wato kananan hukumomin Malam Madori da Hadeja.
Ya ce nan ba da dadewa ba gwamnatin jihar za ta nada kwamashinoni da masu ba Gwamna shawara da sauran mukaman siyasa.
A wani labarin kuma Gwamna Abubakar Badaru ya amince shugabanin gudanarwa na Jami’ar Jihar da ke Kafin Hausa su ci gaba shugabancinsu. Wata sanarwa da ta fito daga Sakataren Gwamnatin Jihar Malam Adamu Abdulkadir Fannani dauke da sanya hannun kakakinsa Malam Mati Ali Unguwar Shuri ce ta bayyana haka.
Gwamnan ya kuma nada Farfesa Abubakar Rasheed a matsayin Uban Jami’ar Jihar kuma Shugaban Gudanarwar Jami’ar. Sauran wakilan hukumar sun hada da Farfesa Jummai Audi da Farfesa Sa’idu Abdu babura da Farfesa Haruna Abdullahi Birniwa.
Sauran sun hada da Shugaban Jami’ar da mataimakinsa da kuma wasu iyayen jami’ar da daya daga cikinsu jami’ar ce za ta zabe shi, yayin da Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi da Ma’aikatar Kudi za su kasance mambobi a kwamatin gudanarwar jami’ar.