Ba zan sake tsayawa takara ba – Shugaban Majalisar Amurka
A wata sanarwar ba zata, Shugaban Majalisar Dokokin Amurka, Paul Ryan ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa takara ba, yana mai cewa yanzu lokaci ya yi da zai koma gefe daya ya zauna da matarsa da ‘ya’yansu uku. Shugaban majalisar wakilan ya sanar da hakan ne bayan ya yi shekaru 20 a majalisar yana […]

A wata sanarwar ba zata, Shugaban Majalisar Dokokin Amurka, Paul Ryan ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa takara ba, yana mai cewa yanzu lokaci ya yi da zai koma gefe daya ya zauna da matarsa da ‘ya’yansu uku.
Shugaban majalisar wakilan ya sanar da hakan ne bayan ya yi shekaru 20 a majalisar yana wakiltar mazabarsa, ya ce ya gaji haka, ba zai yi takarar neman a sake zabensa a zaben da za a yi cikin Watan Nuwamban bana ba, lamarin da ya jawo ayar tambaya, har ma wasu ke kokwanton cewa abu ne mai wuya jam’iyyar Republican ta ci gaba da zama mai rinjaye bayan zaben rabin wa’adin na bana.
Paul Ryan, ya bayyana haka ne a wani taro ya yi da manema labarai a ranar Larabar da ta gabata, inda ya ce zai yi ritaya bayan wannan majalisa ta kammala aikinta a cikin watan Janairun badi. Bayan shekaru 20 a majalisa, Ryan ya ce yana so ya samu lokaci sosai da uwargidansa da kuma ‘ya’yansu uku. Tuni dai ma su fashin baki kan al’umaran yau da kullum ke ganin cewa ritayar da shugaban majalisar zai yi, abu ne da zai janyo zazzafar kamfen tsakanin ‘yan jam’iyyar Republican akan wanda zai maye gurbin nasa.