Ba zan sake tsayawa takara da Ganduje ba – Mataimakin Gwamnan Kano

Mataimkin Gwamnan Jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa takara don yin tafiya tare da shugabansa Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdulalhi Umar ganduje a zaben 2019 ba, inda ya ce da zarar wa’adin mulkinsu ya kare zai tattara kayansa ya koma jami’a don ci gaba da aikinsa na koyarwa. Mataimakin […]

Ba zan sake tsayawa takara da Ganduje ba – Mataimakin Gwamnan Kano

Mataimkin Gwamnan Jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa takara don yin tafiya tare da shugabansa Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdulalhi Umar ganduje a zaben 2019 ba, inda ya ce da zarar wa’adin mulkinsu ya kare zai tattara kayansa ya koma jami’a don ci gaba da aikinsa na koyarwa.

Mataimakin Gwaman ya bayyana wadannan kalamai ne a cikin wani faifan murya da ke yawo a kafafen sada zumunta na yanar sadarwa inda aka ji Gwamnan yana bayyana cewa a maimaikon ya bi bayan Gwamna Ganduje zai marawa tafiyar tsohon Gwamna Dokta Rabiu Musa Kwankwaso baya “dama can Kwankwaso ne ya bayar da sunana aka sa ni a matsayin abokin tafiyar gwamnatin Ganduje, don haka da zarar wa’adin mulkin nan ya kare zan koma Jami’ar Bayero na ci gaba da aikin da aka sanni akansa.”

Malam Usman Bello shi ne Jami’in Hulda da Jama’a na Mataimakin Gwamnan, kuma ya tabbatar da kalaman da Mataimakin Gwamnan ya yi, inda ya ce ya furta su ne a taron da ya yi da magoya bayansa da suka fito daga karamar Hukumar Gwale a Gidan Mambayya.

Kakakin na Matiamkain Gwaman ya kara da cewa “Duk da cewa Mataimakin gwamnan ba shi da wata matsala tsakaninsa da Gwamna Ganduje a tsarin gwamnati, sai dai abin da ake yi a Jam’iyyar APC ne ba ya jin dadinsa musamman cire shugaban jam’iyya a mazabarsa ta Mandawari da Jam’iyyar APC ta jihar ta yi ba tare da neman yardarsa ba”.

Haka kuma a cikin faifan muryar, an ji Mataimakin Gwaman yana  korafin yadda aka canza hotonsa da na wani  inda ya ce “a lokacin yakin neman zaben 2015

zan iya tunawa an sanya hotona tare da na Gwamna da kuma na Muhammadu Buhari, amma a yanzu an maye gurbin hotona da na wani, inda har aka sanya hoton a mahaifata. Me na yi a mahaifata?,  me na yi a mahaifata? Me na yi da na cancanci irin wadannan abubuwa?”

Game da batun tazarce na Gwamna Ganduje, mataimakin gwamnan ya bayyana cewa “wadanda suke son yin tazarce su je su yi abinsu, amma ni addu’ata ita ce na ga na koma jami’a. Ba zan iya ci gaba da zama a wurin da za a zartar da shugabancin jam’iyyata ta APC a mahaifata tare da cire dan’uwana na jini ba tare da wani ya tuntube ni ba”

Mataimakin gwamnan bai fito fili ya soki Gwamna Ganduje ba, sai dai wasu na ganin wasu ‘yan siyasa da ke kusa da gwamnan ba sa son a ci gaba da gudanar da al’amura da shi.

To amma sai dai a wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba ya fitar ta ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi matukar kaduwa da jin bayanan mataimakinsa. “Gwamna ya bayar da umarni a gaggauta mayar da shugaban jam’iyyar da aka cire, kana ya yi kira ga ‘yan siyasa da a kodayaushe su rika tuntubar shugabannin jam’iyya da kuma ‘yan siyasar da ke rike da manyan ofisoshi kafin su aiwatar da wata manufa wacce ka iya jawo ce-ce-ku-ce”, in ji sanarwar.

Gwamnan Ganduje ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa da su rika tuntubar shugabannin jam’iyya da masu rike da manyan mukaman siyasa  kafin su zartar da wani abu makamancin wannan.

Har ila yau Gwamna Ganduje ya yi kira ga ‘yan siyasa da sauran al’ummar jihar da su rika girmama mataimakin gwamnan a duk lokaicn da wata mu’amala ta hada su.

Ko da yake har yanzu Gwamna Ganduje bai fito fili ya ce zai sake tsayawa takara a shekarar 2019 ba, amma masana harkokin siyasa na ganin da wuya ya ce ba zai yi takarar ba kasancewa wannan shi ne wa’adinsa na farko cikin wa’adi biyu da kundin tsarin mulki ya ba shi ikon nema. Haka kuma Farfesa Hafiz Abubakar dai makusanci ne ga tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ke takun saka da Gwamna Ganduje tun bayan zaben 2015.