Ba zan sauka daga Mataimakin Gwamna ba – Mukhtari Shagari
Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Mukhtari Shehu Shagari ya ce ba zai sauka daga kujerar Mataimakin Gwamnan Jihar ba, har zuwa karshen wa’adin mulkinsu. Mataimakin Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Asabar da ta gabata a lokacin da ya kira taron masu ruwa da tsaki a Jam’iyar PDP na jihar a sabuwar sakatariyar jam’iyyar da […]

Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Mukhtari Shehu Shagari ya ce ba zai sauka daga kujerar Mataimakin Gwamnan Jihar ba, har zuwa karshen wa’adin mulkinsu. Mataimakin Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Asabar da ta gabata a lokacin da ya kira taron masu ruwa da tsaki a Jam’iyar PDP na jihar a sabuwar sakatariyar jam’iyyar da ke Unguwar Koko, a karo na farko bayan da Gwamna Wamakko ya koma Jam’iyar APC. Alhaji Mukhtari Shagari ya ce jam’iyyarsu ta PDP kadai ce jam’iyyar siyasar da ya kamata Sakkwatawa su goyi bayanta don tsarinta na son ciyar da jihar da kasa baki daa gaba. Ya ce a jihar kanta sabuwar jam’iyyar ta rabu gida biyu ba a san ta kwarai ba, saboda rashin tsari da manufa mai kyau, kan haka suke ba magoya bayansu tabbacin su ne za mu kafa gwamnati a 2015 insha’Allah. A wurin gangamin jagorori jam’iyyar sun yi jawaban neman a hada kai domin yakar gwamnatin Wamakko, cikinsu akwai Sanata Ilah Gada da Sanata Ladan Shuni da Sanata Abdallah Wali, Jakadan Najeriya a kasar Moroko da shugaban jam’iyyar na farko a jihar Alhaji Arzika Tambuwal da tsohuwar shugabar mata ta PDP, Hajiya Rabi Giyawa da Alhaji Altine Tukur Faru wanda ya yi magana a madadin tsofaffin shugabannin Jam’iyyar PDP na kananan hukumomi. Alhaji Bala Musa Yabo ne ya yi magana a madadin Alhaji Hurumi da Alhaji Gatau ’yan majalisa uku da suka ki barin jam’iyyar, inda ya ce ba za su yi butulci ga PDP ba shi ya sa suka tsaya a jam’iyyar. Wasu jigogin Jam’iyyar APC uku da suka koma PDP, Alhaji Sa’idu Gumburawa da Alhaji Yusuf dahiru Yabo da Alhaji Ibrahim Magaji sun ce sun bar jam’iyyar ce saboda karbar Gwamna Wamakko da jam’iyyar ta yi inda suka ce hakan kasa iya gudanar da dimokuradiyya ce a jam’iyyance.