Ba zan taba barin zuri’ar Shata ta wulakanta ba – Makadin Shata

Nuhu Babanyara, dattijo dan kimanin shekara saba’in da haihuwa, daya ne daga cikin makadan marigayi Dokta Mamman Shata Katsina da suka rage a raye. Yana daya daga cikin makadan da a yanzu haka Khalifan Shata, Muhammad Sanusi Shata ya gada kuma yake tafiyar da sana’arsa ta waka tare da shi. A zantawarsa da Aminiya a […]

Ba zan taba barin zuri’ar Shata ta wulakanta ba – Makadin Shata
Ba zan taba barin zuri’ar Shata ta wulakanta ba – Makadin Shata

Nuhu Babanyara, dattijo dan kimanin shekara saba’in da haihuwa, daya ne daga cikin makadan marigayi Dokta Mamman Shata Katsina da suka rage a raye. Yana daya daga cikin makadan da a yanzu haka Khalifan Shata, Muhammad Sanusi Shata ya gada kuma yake tafiyar da sana’arsa ta waka tare da shi. A zantawarsa da Aminiya a Gombe, makadin ya bayyana cewa duk kasashen nan na Afirika, babu kasar da bai je ba tare da Marigayi Shata. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Dattijo, wane ne Babanyara?
Sunana Nuhu Babanyara Makadin Shata Funtuwa.
Gashi na iske ka kana yi wa Khalifan Shata kida, kafin shi, ko ka taba yi wa shi kansa Shata din kida kuwa kuma idan ka taba yi, shin tun yaushe ka fara?
Wannan Sana’a ta kida dai ni gadarta na yi tun ina karami. Lokacin ina makaranta, gwargwadon karatun da na yi duk da dai gadarta na yi amma Allah Ya kaddara ta nan ne hanyar abincina yake?
Kamar shekara nawa ke nan yanzu?
Eh, in takaice maka dai yanzu zai kai kamar shekara 50 zuwa 55 muna lallabawa, muna cin abinci da ita.
Kasancewar marigayi Mammam Shata Katsina ka yi wa kida kuma an ce duk cikin makadansa saura kai kadai, sauran sun mutu ne ko karfinsu ne ya kare?
A’a, saura mu uku muka rage, daya dan amshi ne, Sani Musawa. Allah Ya jarabce shi da rashin kafa da kuma makanta, yana nan zaune a gida, Musawa Jihar Katsina. Sai kuma abokin kidana, Magaji Mahuta. Shi ma Allah Ya jarabce shi, a duke yake tafiya, ba ya iya komai sai ni Nuhu Babanyara.
A yaran Shata makada, dama kun kai ku nawa ne?
Eh, mu ashirin da uku ne amma yanzu saura mu uku masu Numfashi. Ka ji kuma irin halin da sauran biyun suke ciki, guda ashirin sun kwanta dama.
Kasancewarka makadin Shata, tun kamar yaushe ka fara yi masa kida?
Ina tare da Shata ne tun zamanin mulki tsohon Shugaban kasar Najeriya, Aliyu Shehu Shagari. Da yayyenmu ne a wajen, suka kauce, ni kuma a ranar da aka yi wa Shagari juyin mulki kwanana daya tak da komawa wajen Shata. Muna kuma tare har zuwa lokacin da Allah Ya yi masa rasuwa, ya koma gidansa na gaskiya. Sannan yanzu kuma dansa ya gaje ni.
Kamar yadda ka ce gadon wannan sana’a ta kida ka yi, daga wajen iyayenka ne ko daga yayyenka ka gada?
Eh, daga wajen iyaye ne na gada, domin kakana ya yi kida, mahaifina ma ya yi, sannan yayyena suka yi, ni ma na kama sai dai kuma ni ’ya’yana da na haifa ba su yin kida; sun kama aiki ne irin naku na ’yan boko. Sun kama aiki yanzu, duk da boko suke cin abinci. Ka ga zan ce daga kaina ke nan watakila gado ya kare, sai dai ba mu san wani hukunci na Allah ba amma ni kam har yanzu ina yi. Domin shi wannan yaro gada ta ya yi tun da ni makadin ubansa ne kuma yana yi mini biyayya daidai gwargwado. Ni kuma duk wanda aka ce jinin Shata ne, ba ni yasar da shi, sai dai idan shi ya yasar da ni. Kuma shi Sanusi yana bi na sau da kafa, domin ya dauke ni uba. Zan ce masa yi ya yi, zan ce masa bari ya bari, don haka nake biye da shi. Ina sa shi a hanya, inda na ga zai baude in dawo da shi hanya.
A cikin makadan Shata wa ya fi iya kida, wanda idan ya yi kida yakan tsuma Shata?
Makadan Shata wadanda ba za a yi kamarsu ba su hudu Ne: Ni nan makadi ne wanda na yi wa Shata kida, ni kadai a wasu wakoki da dama amma akwai hudu wadanda ba za a yi kamarsu ba, sai dai a kamanta. Na farko, akwai Tulun Amina sai na biyu Alhaji Mani a Funtuwa yake, sai Alhaji Kuttuku a Kudan yake, sai Sasuwai a Jos yake. Ka ga wadannan hudun har yanzu ba a yi kamarsu ba a fagen kida.
Wace waka ka fara yi wa Shata kida da ita?
Wannan wakar a gaskiya ba zan iya tuna ta ba.
Mene ne gaskiyar cewa duk abin da Shata ya gani nan take zai iya yi masa waka?
Eh, gaskiya ne, domin wannan wata ilhama ce daga Allah. Idan gani ka yi ko wani ne ya gaya maka, to gaskiya ne saboda Shata bai taba rubuta abu ba don zai masa waka. Idan muka je filin waka, a nan Allah zai kawo wakar kuma a nan za mu yi mata kida.
Baba, akwai wata magana da mutane suke fadi, cewa wata rana kun je filin waka, Shata yana waka sai ku makada kida ya gagara; sai ya ce “ya ku na sama ku amsa.” Mene ne gaskiyar wannan batu?
To, wannan duk wanda ya fada ya fada ne shi da Allah, domin ba a taba yin haka ba.
Wace irin bajinta ce Dakta Mammam Shata yake da ita da ake cewa ya gagari sauran mawaka?
Dalili shi ne, kowace irin waka kake yi Shata bai cewa zai yi kamarka sai dai kai ka ce kana so ka zama kamarsa, domin shi wakarsa ya tsaya a kai, bai kwaikwayon wakar wani. Sannan komai ka samu wajen waka shi ba zai maka bakin ciki ba.
A matsayinka na makadin Shata, wadanne kasashe kuka taba zuwa da Shata?
Babu wata kasa a Afirika da Shata bai zagaya da ni kuma ya nuna ni ba, da ma wasu kasashe na duniya ’yan kadan kuma har in tafi kabarina, duk inda na je ina cin arzikin Shata. Ka ga ashe ya yi mani hanyar cin abinci. Saboda haka kullum na yi Sallah sai na yi masa addu’a kuma zuri’arsa ban bari in ga ta wulakantu. Khalifansa kuma rarrafe yake yi, ina taro shi.
Daga karshe mece ce gaskiyar cewa marigayi Shata a lokacin da ya mutu yana da shekaru 76 ne?
Ai dubawa za ka yi ka gani, wane ne ya fada? Domin wanda ya fada din ai uwarsa ma ba ta haife shi ba balle ya san shekarun Shata, kimantawa ya yi irin na masu ilimin boko amma ya fi haka nesa ba kusa ba.