Ba zan yi aure ba sai na kammala makaranta – A’isha Tsamiya
A’isha Aliyu, wacce aka fi sani da lakanin ‘Tsamiya,’ yau shekarunta uku ke nan da fara harkar fim din Hausa, amma sunanta ya zama tamkar ruwan dare gama duniya, musamman ganin yadda ta samu amsuwa ga ’yan kallo. Ta ta’allaka wannan shahara tata ga yadda take maida himma da kokari wajen fuskantar sana’arta. Haka kuma, […]
A’isha Aliyu, wacce aka fi sani da lakanin ‘Tsamiya,’ yau shekarunta uku ke nan da fara harkar fim din Hausa, amma sunanta ya zama tamkar ruwan dare gama duniya, musamman ganin yadda ta samu amsuwa ga ’yan kallo. Ta ta’allaka wannan shahara tata ga yadda take maida himma da kokari wajen fuskantar sana’arta. Haka kuma, ’yar wasan ta bayyana cewa ba za ta yi aure ba har sai ta samu gamsasshen ilimi, ke nan bayan ta kammala makaranta.
Ga shi kin samu amsuwa a harkar fina-finan Hausa, yaya haka ta faro?
A lokacin da na kudurta cewa in fara harkar fim din Hausa, ban taba tsammanin zan shahara ba cikin kankanen lokaci. Amma bayan da fim dina na dakin Amarya ya fito, shi ke nan sai sunana ya daukaka, na samu amsuwa. Daga nan ne fa sai furodusoshi suka yi ta ribibina, suna saka ni a fina-finansu. Ai fa shi ke nan sai na zama ko’ina an san ni, ta kai ga babu yadda za a yi in shiga wani wuri ba tare da masoya suna kula ni ba. Za ka ji suna kiran sunana, musamman ma idan na shiga kasuwa ko wata matattarar jama’a. Na zama ko’ina a Arewacin Najeriya an san ni kuma ana kauna ta.
Wadanne fina-finai ne suka zama linzamin nasararki?
Fina-finai biyu, wato fim din So da dakin Amarya, su ne suka zama silar shahara ta. Na ta’allaka nasarar kuwa ga darakta, domin kuwa na sanya wa raina cewa bari in yi iyaka kokarina wajen bin umurnin duk da daraktana ya ba ni. Lokacin da fina-finan biyu suka fita, na sanya ina kallo, sai na yi ta mamakin kaina, na ga kamar ma ba ni ba ce ke yin wannan wasa. Babu shakka na yi matukar gamsuwa kuma na yi mamakin yadda na fito a fim din dakin Amarya. Haka kuma na ji dadin yin wasa tare da manyan ’yan wasa, kamar Ali Nuhu da Halima Atete.
Fim din So shi ne ma na fi kauna, musamman inda na fito tare da shahararren dan wasa, Adam Zango. Babu shakka fim din ya kayatar, musamman ma na gamsu ne da labarin fim din, wanda nake ganin kamar gaskiya ne, ba kirkirarre ba.
Me ya ja ra’ayinki ga harkar fim?
Babban abin da ya ja hankalina kuma na ji ina son shiga harkar fim shi ne, domin ina son in shahara, musamman domin in zama mai taimakon gajiyayyu da mabukata. A rayuwata, ba na gajiyawa da yin kyauta ga mabukata. Na fito daga cikin al’ummar da ke cikin wahala da bukata, don haka ya zama wajibi a kaina in taimaka masu da abin da Allah Ya hore mani ga mabukata. Nakan bayar da abinci da tufafi da kudi ga mabukata a inda nake zaune, wato Kano, kamar kuma yadda nake ziyartar sansanin ’yan gudun hijira da ke nan Kano. Na yi haka a lokacin azumin Ramadan, musamman domin mutanen su samu saukin ibada. Duk da cewa ni ba attajira ba ce amma dai ta sana’ar da nake ta fim, nakan samu dan abin da zan agaza wa gajiyayyu da mabukata, komai kankantarsa.
Me ke burinki a wannan harka ta fim?
Duk da cewa ina samun nasara a fagen wasan fim, babban burina a harkar nan shi ne in zama darakta, mai ba da umurni a fina-finai, kamar dai yadda Muhibbat Abdussalam take yi. Ina da burin in ci gaba da karatu, domin zurfafa ilimina. A yanzu haka na samu shiga Jami’ar North-West da ke Kano. Ina bukatar in samu isasshen ilimi, kafin daga bisani in yi aure. Amma duk da haka na dogara ga Allah kuma na yadda da kaddara, wanda al’amarin na iya canzawa, yadda Allah Ya so. babu mamaki a kan haka in samu mijin da ya dace, kafin in kai ga kammala karatuna. Amma dai burina in kammala tukunna kafin in yi aure.