Ba zan yi karya don a zabe ni Sanata ba –A’ishatu Rasheed

Hajiya A’ishatu Laraba Abdulkadir Rasheed, ’yar marigayi Sarkin Dukku Alhaji Abdulkadir Haruna Rasheed ne, kuma tsohuwar mai bai wa Gwamnan Jihar Gombe shawara ce a bangaren harkokin siyasa, yanzu kuma babbar mai taimaka wa Gwamnan a bangaren harkokin mata, a hirarta da wakilinmu ta ce ba za ta yi karya ga jama’a ba, don a […]

Ba zan yi karya don a zabe ni Sanata ba –A’ishatu Rasheed
Ba zan yi karya don a zabe ni Sanata ba –A’ishatu Rasheed

Hajiya A’ishatu Laraba Abdulkadir Rasheed, ’yar marigayi Sarkin Dukku Alhaji Abdulkadir Haruna Rasheed ne, kuma tsohuwar mai bai wa Gwamnan Jihar Gombe shawara ce a bangaren harkokin siyasa, yanzu kuma babbar mai taimaka wa Gwamnan a bangaren harkokin mata, a hirarta da wakilinmu ta ce ba za ta yi karya ga jama’a ba, don a zabe ta a mukamin Sanata daga mazabar Gombe ta Arewa a karkashin Jam’iyyar PDP ba:

Aminiya: Mene ne dalilanki na tsayawa takarar kujerar Sanata daga Gombe ta Arewa?
A’ishatu A. Rasheed: A matsayina na mace wacce ta fito daga babban gida na sarauta kuma ganin cewa mace ba ta sarauta duk da ma dai ita ta fi sanin damuwar mutane kasancewarta uwa shi ya sa nake son in ga na ba da gudunmawata ga jihata da mazabata Gombe ta Arewa, shi ya sa na yanke shawarar tsayawa takarar Sanata domin idan na ci zabe al’ummata su amfana.
Aminiya: Wasu na ganin shari’a ba ta yarda mace ta shugabanci al’umma ba ba ki ganin za ki samu cikas ganin kuma akwai ’yan takara fiye da goma daga yankin?
A’ishatu A. Rasheed: Gani na yi kamar yadda na gaya maka na fito daga babban gida kuma na samu ilimi shi ya sa nake ganin in fito in tsaya takara ba laifi ba ne, domin addini bai hana ba, saboda shiga siyasa ko yin takara ko rike wani matsayi ba shugabanci (na kololuwa) ba ne, jagoranci ne kuma shari’a ba ta haramta wa mace ba, wannan dama ce ta mace idan ta samu ta kwato wa jama’arta ’yancinsu wannan shari’a ba ta hana ba.
Aminiya: Idan kika samu nasarar zama Sanata a 2015 mene ne burinki ga al’ummar Gombe ta Arewa?
A’ishatu A. Rasheed: Idan Allah Ya ba ni sa’a na zama Sanata zan kawo ci gaba mai ma’ana wajen samar wa matasa sana’oin hannu da kuma hanyoyin dogaro da kansu kuma in sama wa ’ya’yan marasa galihu tallafin karatu (Sponsorship ba Scholarship ba) daga makarantun firamare da karama da babbar sakandare har zuwa jami’a, nan ma ba masu yawa zan dauka ba daidai karfin aljihuna zan dauka ka san tallafi ya bambanta da daukar nauyi gaba daya ko, yauwa ni tallafi zan rika bayarwa domin ba zan dauki abu da yawa in zama makaryaciya daga baya ba, kuma zan bullo da wata hanya ta koya wa mata sana’o’i kamar yadda Uwargidan Gwamna Hajiya Adama Ibrahim dankwambo take yi na koya musu dinki da kiwon kaji da gyaran kai da sauransu.
Aminiya: Ba kowane dan siyasa ne yake daukar alkawari a lokacin neman zabe ya cika ba, wane tabbaci kike da shi don ganin in aka ba ki dama za ki cika alkawuran da kika dauka?
A’ishatu A. Rasheed: Na san Allah Shi ke ba da ikon cika alkawari, amma a matsayina na mace ina tabbatar maka cewa da wuya in yi karya saboda mata suna da rikon amana da cika alkawari fiye da maza. Yanzu misali a yankin Gombe ta Kudu muna da mace da take Majalisar Wakilai tana kamantawa wanda ba duk abin da take yi ne ta dauki alkawuransu ba, wasu abubuwan ma da take yi ba ta dauki alkawarin za ta yi su ba, amma take yi. Sannan Bahaushe ya ce zanen dutse ne yadda na tashi a babban gida tun a baya nake kamanta tallafa wa masu karamin karfi, me zai sa yanzu idan na samu matsayi kuma in canja halina? Ina ganin zan iya cika duk alkawuran da zan dauka in sha Allah.
Aminiya: Wane shiri kika yi don fuskantar zaben ganin cewa bai wuce ’yan watanni ba a gudanar ba?
A’ishatu A. Rasheed: A matsayina na wacce take harkar siyasa tun da jimawa inda a baya na zama mai bai wa Gwamna shawara kan harkokin siyasa na shekara uku, yanzu kuma ina babbar mai taimaka wa Gwamna a kan harkokin mata hakan ya sa ni shiga wasu harkokin siyasar ana damawa da ni kai-tsaye, na san gwagwarmayar da ake yi don haka na shirya tsaf kuma wani abu shi ne jama’a sun fara gane bambancin siyasar kudi da ta akida, yanzu jama’a cancanta suke bi ba kudi ba. Kuma gaskiya na samu karbuwa a wannan yanki nawa domin alherin da na saba shi nake ci gaba da yi wa jama’ata ban canja ba. A kananan hukumomin da suke yankin na kafa kwamitoci biyar kowane na raba musu aikin da za su gudanar don yakin neman zabena.
Aminiya: Kasancewar Kwamishinanki na Aikin Gona da kuke tare da shi yana neman wannan kujera ta Sanata a jam’iyyarku ta PDP ba ki ganin hakan zai kawo muku rarrabuwar kai?
A’ishatu A. Rasheed: A’a ba za mu samu kowace irin matsala da shi ba, domin siyasa ba gaba ba ce, a lokacin da na fito neman wannan takara sai da na nemi goyon bayansa duk da na san shi ma yana neman
wannan kujera. Batun aiki kuma a ma’aikatar aikin gona ai tuni na bari saboda na ga mutane suna neman hada mu, amma sun ki yarda na bar aikin shi ne suka ce in zauna ina taimakawa na zauna din ne kawai saboda na san aikin Gwamna nake yi.
Aminiya: A karshe mene ne kiranki ga ’ya’yan jam’iyyarku ta PDP da kuma magoya bayanki?
A’ishatu A. Rasheed: Kirana ga magoya bayanmu shi ne a hada kai a yi siyasa mai tsabta ban da gaba, kowa ya yi kokari ya tallata dan takararsa ban da fadace-fadace da kashe-kashe domin koda a jihar gaba daya ko kokarin Gwamnan ne yanzu haka babu siyasar cin zarafi ko ta sare-sare a gari kuma kowa ya bi umarnin jam’iyya idan aka gudanar da zaben fitar da gwani mu hadu mu goya wa wanda ya ci baya, don kai jam’iyyarmu ta PDP ga nasarar cin zabe.