Ba zan yi mulkin kama-karya ba – Tinubu

Ya ce zai yi shugabanci daidai da bukatun ‘yan Najeriya

Ba zan yi mulkin kama-karya ba – Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin yin mulkin da ’yan Najeriya za su yi na’am da shi, ba na kama-karya ba.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi bayan an rantsar da shi a matsayin Shugaban Najeriya na 16 a filin taro na Eagle Square da ke Abuja ranar Litinin.

A cewarsa, “Za mu rika tuntuba tare da jin ra’ayin jama’a, amma ba za mu taba yi musu mulkin kama-karya ba. Za mu rika sauraron kowa, kuma ba za mu taba kaskantar da wani ba saboda yana da ra’ayi sabanin namu.

“Mun zo ne mu magance kalubalen Najeriya mu warkar da ita, ba wai mu fama mata ciwonta ba.”

Tinubu, wanda shi ne ya yi wa jam’iyyar APC takara a zaben watan Fabrairun da ya gabata, ya ce an fafata a zaben sosai, amma ya lashe shi bisa adalci.

“Tun da aka dawo mulkin Dimokuradiyya a 1999, Najeriya ba ta taba yi sahihin zabe ba irin wanda na lashe. Sakamakon shi ya nuna abin da jama’a suke so, amma nasarata ba tana nufin na fi kowa ba ne, ko kuma tana nufin ’yan adawata ba su kai matsayina ba,” in ji sabon Shugaban Kasar.

Sai dai ya ce biyan tallafin man fetur ya zama tarihi a Najeriya, sannan ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin kasar cikin kankanin lokaci.