Ba zan yi murabus ba – Shugabar Brazil
Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ta ce ba za tayi murabus ba, bayan da ‘yan majalisar wakilan kasar suka kada kuri’ar amincewa da tsige ta.Yayin da take magana da kafafan yada labarai a Brasilia babban birnin kasar, Misis Rousseff , ta ce ta fusata kan yadda masu adawa da ita ke jifanta da munanan kalamai […]
Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ta ce ba za tayi murabus ba, bayan da ‘yan majalisar wakilan kasar suka kada kuri’ar amincewa da tsige ta.
Yayin da take magana da kafafan yada labarai a Brasilia babban birnin kasar, Misis Rousseff , ta ce ta fusata kan yadda masu adawa da ita ke jifanta da munanan kalamai a lokacin da ’yan majalisar wakilai ke kada kuri’a ranar Lahadi. ’Yan majalisar 367 cikin 513 suna goyon bayan tsigeta.
Ta jajirce a kan cewa ba ta aikata laifin cin hanci ba, kuma babu wasu dalilai na shari’a da za su sa a tsige ta.
Ana dai zargin shugabar ce da sauya kididdigar kasafin kudin kasar don taimakawa kan ta wajen sake tsayawa zabe a shekarar 2014.
Nan da makonni masu zuwa ne ake sa ran gabatar da matakin tsige ta a Majalisar Dattawan kasar, kamar yadda BBC ta bayyana.
Sai dai shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Jakues Wagner ya ce gwamnatinsu tana da karfin gwiwar cewa majalisar dattawa za ta yi watsi da batun tsige shugabar, inda ya ce batun koma baya ne ga dimukradiyya kuma lamarin wani abu ne da wadanda suka ki amincewa da zabenta a shekarar 2014 suka kitsa.