Ba zan yi wa harkar shari’a katsa-landan ba — Tinubu

Tinubu ya ce zai bai wa ɓangaren shari’a damar gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.

Ba zan yi wa harkar shari’a katsa-landan ba — Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta kare ’yanci da martabar harkar shari’a, ta hanyar kaucewa yi wa ɓangare katsa-landan.

A wajen rantsuwar Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, wanda yanzu haka uta ce shugabar kotun koli ta Najeriya (CJN) ta 23, Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta girmama ɓangaren gudanarwa da shari’a.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi katsa-landan kan aikace-aikacen wasu ɓangarorin gwamnati ba.

Wannan taron ya gudana a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin.

“Shari’a na daga cikin muhimman ginshiƙai na dimokuraɗiyyarmu,” in ji Tinubu.

“Ɓangaren shari’a na Najeriya yana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da kowa yana da haƙƙi.”

Ya bayyana cewa shari’a ita ce mafita ta ƙarshe ga talakawa, tana ba su tabbacin cewa za su iya neman adalci idan an cutar da su.

’Yana da muhimmanci shari’a ta kasance mai ’yanci,” a cewarsa.

“Na yi alƙawarin kare ingancinta.”

Duk da cewa ya amince cewa ɓangarorin gwamnati na iya aiki tare, ya jaddada muhimmancin girmama rawar da kowane ɓangare yake takawa.

“Ba za mu yi katsa-landan kan dangantakar da ke tsakanin waɗannan ɓangarori na gwamnati ba.”

Tinubu ya yi kira ga Mai Shari’a Kekere-Ekun da ta ci gaba da nuna shugabanci na gari, jarumtaka, da gaskiya a aikinta.

Ya kuma bayyana, “Ɓangaren shari’a na Najeriya yana buƙatar shugaba mai waɗannan halaye a wannan lokaci, kuma na yarda za ku zama abin koyi ga wasu.”

Mai Shari’a Kekere-Ekun yanzu haka ita ce mace ta biyu da ta taɓa zama shugabar kotun koli a tarihin Najeriya.