Ba zan zama dan amshin shata a majalisa ba – Dokta Yahaya
Sanata mai wakiltar Kebbi ta Arewa Dokta Yahaya Abdullahi, ya ce ba zai zama dan amshin shata a Majalisar Dattawa ba, duk da cewa wannan ne karo na farko na zuwansa majalisar.Sanata Yahaya Abdullahi, ya bayyana haka ne a taron manema labarai da ya kira a masaukin Shugaban kasa da ke Birnin Kebbi, inda ya […]
Sanata mai wakiltar Kebbi ta Arewa Dokta Yahaya Abdullahi, ya ce ba zai zama dan amshin shata a Majalisar Dattawa ba, duk da cewa wannan ne karo na farko na zuwansa majalisar.
Sanata Yahaya Abdullahi, ya bayyana haka ne a taron manema labarai da ya kira a masaukin Shugaban kasa da ke Birnin Kebbi, inda ya ce jama’ar yankin Kebbi ta Arewa sun zabe shi ne domin ya je ya wakilce su a majalisar, saboda sun ga ya cancanta domin ya kwato musu hakkinsu. Ya ce da yarda Allah ba zai zama dan kallon a majalisar ba duk inda hakkinsu yake sai karfinsa ya kare wajen nemowa.
Sanatan ya ce, suna cikin wani yanayi na aiki, wanda ya zama dole su zauna su tantance gaskiya da akasinta, kuma hakkinsu ne a yanzu su sa Jihar Kebbi a gaba ba yankinsu kadai ba, saboda matasa sun samu aikin yi a kuma samu karin zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare da bai wa gwamnatin jihar shawarwari masu ma’ana domin ci gaban jihar.
“Kuma ina tabbatar wa jama’a za mu yi aikinmu tsakani da Allah. Duk inda muka ga za a yi ba daidai ba, za mu fadakar, don a yi yadda ya kamata, a shirye nake in mika dukkan koke-koke da bukatun jama’ar yankina ga inda ya kamata,” inji shi.
Sai ya yi kira ga jama’ar da suka zabe su cewa kofarsu a bude take domin karbar shawararsu, kuma a gaya musu laifinsu idan suka yi, saboda tana iya yiwuwa idan sun bayar da dalilinsu na daukar wani mataki jama’a su gamsu. “Amma ba daidai ba ne idan mun yi kuskure a je a yi ta gulma da batunci a gefe. Dole a rika ba mu shawara don mu tafiyar da al’amarin wakilcin jama’a yadda ya dace,” inji Sanatan.
Ya ce dukkansu ’yan Majalisar Dattawa suna goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari a kan yaki da cin hanci da rashawa dari bisa dari, kuma ya ce suna da yakinin dukkan wadanda aka samu da laifi ba kawai za a kwace ko su sallamar da duk kadarorin da suka mallaka ga gwamnati ba ne dole ne a hukunta su bayan an karbe dukiyar jama’a daga hannunsu.