Ba’a narka kitsen mushe, kuma ba a sayar da bargonsa
BABI NA dARI DA HUdU:-Ba’a narka kitsen mushe, kuma ba a sayar da bargonsa.Jabir Allah Ya yarda da shi ya ruwaito shi daga Annabi (SAW).” 665. An karbo daga Humaidiyu ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Amru dan Dinar ya ba mu labari ya ce, dawus ya ba ni labari cewa: Lallai […]
BABI NA dARI DA HUdU:-
Ba’a narka kitsen mushe, kuma ba a sayar da bargonsa.Jabir Allah Ya yarda da shi ya ruwaito shi daga Annabi (SAW).”
665. An karbo daga Humaidiyu ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Amru dan Dinar ya ba mu labari ya ce, dawus ya ba ni labari cewa: Lallai shi ya ji dan Abbas Allah Ya yarda da su yana cewa: “Labari ya isa ga Umar cewa, lallai wani ya sayar da giya, sai ya ce: “Allah Ya la’ani wane, shin bai sani cewa, lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Allah Ya la’ani Yahudawa da aka haramta musu kitse sai suka dauke ta suka sayar.”
666. An karbo daga Abdan ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Yunus ya ba mu labari daga dan Shihab ya ce, “Na ji Sa’id danMusayyib ya ce, daga Abihuraira Allah Ya yarda da shi cewa: “Hakika Manzon Allah (SAW) ya ce, “Allah Ya la’ani Yahudawa, da aka haramta musu cin kitse sai suka sayarda ita, suka ci kudinta.” Abu Abdullahi (Bukhari) ya ce, “Allah Ya la’ane su, ya tsine musu, kamar yanda ya ce: “An la’ani masu kirkiren karya, wato an tsine wa masu kirkiran karya.”
BABI NA dARI DA BIYAR:-
Sayar da hotuna wadanda ba su da rai. Da bayanin abin da aka hana game da haka.
667. An karbo daga Abdullahi dan Abdul Wahab ya ce: “Yazid dan Zurai’u ya ba mu labari ya ce, Aufu ya ba mu labari daga Sa’id dan Abil Hasan ya ce: “Na kasance a wurin dan Abbas Allah Ya yarda da su, lokacin da wani mutum ya shigo ya ce: “Ya Baban Abbas, lallai ni, mutum ne wanda abincina ke bisa sana’ar hannuna, kuma lallai ni, ina yin wadannan hotuna.” Sai dan Abbas ya ce: “Ba zan baka labari ba face wanda na ji daga Manzon Allah (SAW) na ji shi yana cewa: “Wanda duk ya suranta wani hoto, to lallai Allah zai azabtar da shi har sai (an ce,) ya hura masa rai, alhali shi ba mai hura rai ba ne. Sai mutumin ya firgita, firgita mai tsanani fuskarsa ta yi ja (kamar rawaya).” Sai (dan Abbas) ya ce, “Kaitonka! idan ka ki face sai ka ci gaba da aikatawa, to na horeka da yin hotunan wannan itaciya, da dukkan abin da babu rai cikinsa.” Abu Abdullahi (Bukhari) ya ce, “Sai’id dan Abi Arubat ya ji daga Nadar dan Anas da wannan sau daya.
BABI NA dARI DA SHIDA:-
Haramcin sayar (cinikin) giya. Jabir Allah Ya yarda da shi ya ce, “Annabi (SAW) ya haramta cinikin giya.”
668. An karbo daga Muslim ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga A’amashi daga Abi Duhah daga Masruk daga A’ishat Allah Ya yarda da ita, cewa: “Lokacin karshen ayoyin suratul Bakara suka sauka, sai Annabi (SAW) ya fita zuwa ga mutane. Ya ce, “An haramta cinikin giya.”