Ba’Amurke ya kashe miliyan 28 don ya koma kamar ’yar kwalisa Kim Kardashian

Wani Ba’Amurke, mai suna Jordan James Parke da ke matukar kaunar ’yar Kwalisa tauraruwar shirin talabijin a Amurka, Kim Kardashian, ya kashe Dalar Amurka dubu 150, wato daidai da Naira miliyan 28 da dubu 50, don a sauya masa siffarsa, yadda kamarsa za ta koma tamkar ta wannan ’yar kwalisa.’Yar kwalisa Kim ta sha fitowa […]

Ba’Amurke ya kashe miliyan 28 don ya koma kamar ’yar kwalisa Kim Kardashian
Ba’Amurke ya kashe miliyan 28 don ya koma kamar ’yar kwalisa Kim Kardashian

Wani Ba’Amurke, mai suna Jordan James Parke da ke matukar kaunar ’yar Kwalisa tauraruwar shirin talabijin a Amurka, Kim Kardashian, ya kashe Dalar Amurka dubu 150, wato daidai da Naira miliyan 28 da dubu 50, don a sauya masa siffarsa, yadda kamarsa za ta koma tamkar ta wannan ’yar kwalisa.
’Yar kwalisa Kim ta sha fitowa a shafukan mujallu da shiryen-shiryen talabijin da ake tallata hajar tufafin ado da kayan kwalliya, don haka ba abin mamaki ba ne idan har Parke na kaunar zama mai siffa irin ta Kim.
Wani gwanin zayyanar kwalliya dan Birtaniya, ya yi matukar kokari ya yi, wajen fito da samfurin siffar Kim, inda ya yi amfani da kayan shafe-shafe har nau’uka 50 da jan baki da abin tsawaita muka-muki da kawata idanu da kuma abin cire gashi, kamar yadda jaridar dailymail.,co.uk ta ruwaito a shafinta na sadarwa.
Parke ya bayyana wa jaridar The Sun cewa yana matukar kaunar Kim ’yar shekara 33, bayana da ya kalli wnai shgirin talabijin mai taken “Kasance tare da iyalan Kardashian – Keeping Up With The Kardashians.”
“Ina matukar  kaunar komai game da Kim. Ita ce mace mafi kyau da na taba gani. Fatar jikinta na da kyau, ga gashinta da komai nata,” inji shi.