Ba’Amurkiya ta ajiye aiki ta hanyar rawa

Wata Ba’Amurkiya da ke aiki a tashar labarai, a wani kamfanin bidiyo da ke kasar Taiwan, ta ajiye aikinta ta hanyar yin rawar minti biyu da ke nuni da barin aikin.A cikin hoton bidiyon da ta aike wa kamfani, an nuna Marina Shifrin na mika takardar ajiye aiki, a lokacin da take taka rawar kidan […]

Ba’Amurkiya ta ajiye aiki ta hanyar rawa

Shifrin a lokacin d atake rawar ajiye aikiWata Ba’Amurkiya da ke aiki a tashar labarai, a wani kamfanin bidiyo da ke kasar Taiwan, ta ajiye aikinta ta hanyar yin rawar minti biyu da ke nuni da barin aikin.
A cikin hoton bidiyon da ta aike wa kamfani, an nuna Marina Shifrin na mika takardar ajiye aiki, a lokacin da take taka rawar kidan mawaki Kanye West “Gone – Ya tafi.” A lokacin da take rawar, sai aka rika nuna sakonni a kasar hoton da ke bayyana manufarta.
“tsawon shekara biyu na sarayar da soyayyata da lokacina da karfina saboda wannan aiki,” kamar yadda Shifrin ta rubuta a kasar hoton da take rawa. “Shi kuwa shugabana babu abin da ya damu da shi sai yawan aiki, mutane nawa aka jawo hankalinsu suka kalli hoton bidiyonmu. Don haka na ga ya fi dacewa ni ma in yi wa kaina hoton bidiyo daya na kaina,” inji ta.
“To na gano…” a cewarta, “ Zan yi wa kaina bidiyo guda na kashin kaina. Zan mayar da hankali a kansa, maimakon damuwa da ra’ayoyi ba.”
Abin mamaki shi ne, wannan bidiyo na ta ya watsu ko’ina, har ya jawo hankalin masu kallo, mutum dubu 450.
Shugaban wurin aikin nata bai ce komai game da al’amarin ba. Shifrin dai tuni ta koma kasar Amurka a ta tara dimbin mabiya a shafin sadarwarrta na tweeter.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan