Baba an iya loma amma ba a iya kai nika ba!

Wani yaro ne ya dawo gida ya samu mahaifinsa yana cin abinci. Sai ya dubi mahaifin ya ce, “Su Baba an iya loma amma ba a iya kai nika ba!” Daga Ummu Safiyya, 08105657565  Aradu ban yi sanyi ba! Wani Bafulatani ne ya yi laifi ’yan sanda suka biyo shi da gudu. Yana zuwa wajen […]

Baba an iya loma amma ba a iya kai nika ba!

Mu sha dariya

Wani yaro ne ya dawo gida ya samu mahaifinsa yana cin abinci. Sai ya dubi mahaifin ya ce, “Su Baba an iya loma amma ba a iya kai nika ba!”

Daga Ummu Safiyya, 08105657565 

Aradu ban yi sanyi ba!

Wani Bafulatani ne ya yi laifi ’yan sanda suka biyo shi da gudu. Yana zuwa wajen wani mai gyaran firiji sai ya bude daya ya shige ciki ya rufe. Ashe wani dan sanda ya gan shi, yana zuwa sai ya kwankwasa firijin Ya ce: “Wane ne a ciki?” Sai Bafulatanin ya ce: “Kunun aya ne da zobo.”

Sai dan sandan ya ce “Fito mu sha.” Sai Bafulatanin ya ce: “Aradu ban yi sanyi ba!”

Daga Alhaji Umar Foreber, Gashuwa

Budurwar Baba ce!

Wani yaro ne mahaifiyarsa ta kira shi tana masa tambayoyi a kan karatunsa na boko, sai ta ce wane ne sunan Shugaban da ya mika wa Buhari mulki? Sai yaron ya ce Mama na sani Obasanjo ne. Sai ta ce ka ji wawa, Jonathan ne, don haka ka kula da karatunka. Shi kuma yaron ya ce, to Mama ke kuma ga tambaya, wace ce Anty Jamila? Sai mahaifiyar ta ce ban sani ba, sai yaron ya ce wawiya ki kula da aurenki budurwar Baba ce!

Na manto mabudin dakinmu a cikin mota!

Wadansu ’yan Najeriya ne su uku suka je China aka sauke su a bene mai hawa 100, dakinsu yana hawa na 60, ran nan sun je yawo sai suka yiwo dare suka zo suka tarar na’ura ta tashi aiki sai dai su hau da kafa har hawa 60 inda dakinsu yake. Sai suka yi dabarar daya ya yi ta ba su labarin al’ajabi har zuwa hawa na 20, na biyu ya ba su na ban-dariya zuwa hawa na 40 na ukun kuma ya yi ta ba su labarin ban haushi zuwa hawa na 60 din.

Haka suka yi ta yi har hawa na 40 inda mai ba da labarin ban haushi zai fara, aka ce saura kai, sai ya fara da cewa “Labarin ban haushin da zan fara da shi, shi ne na manto mabudin dakin namu a cikin mota a can kasa!”

Labarai daga 09099886988