Baba Goni: Yaron da ya taimaka aka kubutar da ’yan matan Chibok biyu

Wani yaro dan shekara 15 mai siuna Baba Goni ya taimaka wajen ganowa da kubutar da biyu daga cikin ’yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace fiye da mako biyar da suka gabata, lokacin da ya jagoranci ’yan bangar da ake kira da Sibiliyan JTF suka shiga daji domin farauto ’yan matan.’Yan matan […]

Baba Goni: Yaron da ya taimaka aka kubutar da ’yan matan Chibok biyu
Baba Goni: Yaron da ya taimaka aka kubutar da ’yan matan Chibok biyu

Baba Goni, yaron da ya taimaka aka kubutar da ’yan matan Chibok biyuWani yaro dan shekara 15 mai siuna Baba Goni ya taimaka wajen ganowa da kubutar da biyu daga cikin ’yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace fiye da mako biyar da suka gabata, lokacin da ya jagoranci ’yan bangar da ake kira da Sibiliyan JTF suka shiga daji domin farauto ’yan matan.
’Yan matan biyu, an iske su ne cikin kayan makarantarsu daure a jikin bishiyoyi inda aka tafi aka bar su a cikin daji don su mutu a haka.
 ’Yan matan, wadanda ake zargin an yi musu fyade kuma aka shiga da su cikin dajin an iske su da ransu cikin tsananin zafin rana. “Suna zaune a kasa daure a jikin bishiyoyi a kafafunsu ta gaba – da kyar suke numfashi,” inji Baba Goni, wanda ya yi aiki a matsayin jagora ga tawagar ’yan bangar da suka shiga dajin don nemo ’yan matan da yanzu suka zama abin tattaunawa a kansu a duniya.
Baba Goni da ’yan bangar sun gano ’yan matan ne mako daya bayan sace su a ranar 15 ga Afrilu a cikin daji kusa da kauyen Ba’ale, tafiyar kimanin awa daya daga garin Chibok, inda aka sace ’yan mata 276 da suke tsakanin shekara 16 zuwa 18, daga makarantar sakandare.
Bayan kwanaki da bacewarsu, kungiyoyin da ke dauke da mutane marasa karfi irin su Baba da suka rika zagawa a dajin cikin motocin a-kori-kura ne suka yi ta kokarin ceto ’yan matan.
 A cewar Baba da dama ’yan matan sun yanke kauna, lokacin da shi da tawagarsa suka tattauna da firgitattun mazauna kauyukan da ’yan Boko Haram suka yi sansani tare da ’yan matan da suka sace na tsawon kwana uku.
Ya ce mazauna kauyukan sun gaya masa cewa ’yan bindigar sun harbe ’yan mata hudu saboda ‘taurin kansu,’ inda suka yi gaggawar binne su, kafin su dauke su zuwa gaba.
Ya kara da cewa: “Duk wanda muka yi magana da shi cike yake da tsoro, suna tsoron fitowa daga gidajensu. Kuma sun ki gwada mana kabarin, sun dai nuna ta inda suka bi.”
Lokacin da Baba da sauran ’yan bangar suka bi sawunsu ne, suka iske ’yan matan biyu, kuma Baba wanda shi ne karaminsu ya tsaya a daidai lokacin abokansa suka dauki mataki. “Sun yi amfani da wuka wajen yanke igiyar da aka daure su. Kuma na ji ’yan matan suna kuka suna gaya wa sauran ’yan bangar cewa an yi musu fyade kafin a tafi a bar su.” Tare suke da sauran ’yan matan da aka sato daga Chibok, wadanda wasu cikin kakin soja suka sace su daga makaranta a tsakiyar dare.
Baba ya ci gaba da cewa: “Babu abin da za iya yi musu. Kuma ba su son yin magana ga mutane. Abin da muka iya yi musu shi ne samo musu motar da za ta kai su ga ’yan sanda a Damboa. Ba su magana, sun dai rike juna ne kawai suna kuka.”
Baba wanda dan wani karamin manomi ne, ya ce bai taba barin kauye ba, kuma hankalinsa ya tashi lokacin da ya ga kananan ’yan matan da ya sani sosai, ’yan ta’adda sun lalata su.
Baba Goni wanda Muslim ne kuma Babarbare da ke da tsaga irin ta Barebari, ana yi masa lakabi da “karami,” saboda yanayin jikinsa, ya ce yakan fita harbin tsuntsaye da abokansa, ko ya fita fatsa da kugiya tare da abokansa, yayin da damina yake taya mahaifinsa aikin gona.
Ya ce shi da ’yan uwansa suna halartar makarantar allo, kuma bai zuwa makarantar boko, kuma yana da shekara 10 a duniya ne harkokin Boko Haram suka kankama a yankinsu, inda suka rika fashi a bankuna don samun kudin gudanar da harkokinsu.
Ya ce, wata rana yana barci a gidansu na laka a kauyen, sai ’yan bindigar suka rika bin daki-daki suna farautar masu fallasa su ga jami’an tsaro. “Na ji surutu, sai na farka nag a mutane suna shigowa ta kofa, inda suka harbi baffana, wanda ke kwace a kan gado kusa da ni. Wannan ne karshen yarintata, karshen komai. Na gan shi kwance cikin jini, sai na juya inda ’yan bindigar suka nuna min bindiga. Sun kama ni da karfi suka dauke ni zuwa waje suka sanya ni a a-kori-kura,” inji shi. Ya ce ya zauna tare da ’yan Boko Haram din na shekara biyu a dajin Sambisa.
Kuma ya ce da dama daga cikinsu suna tare da mata da suke zuwa a kashin kansu har sansanin. Kuma bai taba ganin an sato wata budurwa ba, don haka wannan sabon lamari ne a gare shi. “Akwai samarin da aka sato, amma ba ’yan mata. Duk muna tsoron mutuwa don haka muke yin duk abin da aka umarce mu – kamar debo ruwa da yiwo itace da goge makamai.”
Baba Goni ya kara da cewa: “Ba damar mu yi abokai –don ba ka san wanda za ka amince masa ba. An sanya na rika barci a cikin tsofaffi daga cikin ’yan Boko Haram, manyan masu wa’azi. Ba ni da mai gida a sansanin, kowa yana iya ba ni umarni. Wadannan mutane suna Sallah sau biyar kullum, amma sai su hau baburansu su rika kashe mutane. Na san sun fara ne a matsayin mutanen kirki, amma yanzu ina kallonsu a matsayin mabarnata da suke dauke da bindigogi shake da harsasai.”
Ya ce an koya masa sarrafa bindiga AK-47, bayan ya fara tasawa da kuma yadda zai kwance ya hada ta. Ya ce duk da ba su shan giya ko kwaya, wani lokaci yakan ga suna shan wiwi, kuma yana yi musu kallon mahaukata da a kullum ke tsara yadda za su kai hari na gaba.
Baba Goni ya ce wata rana sai aka ce za a gwada biyayyrsa ga kungiyar, inda kwamandansu ya hada shi da manyansa biyu ya ce, “Mu je gidanmu in harbi mahaifna.” Kuma sun hau babur zuwa kauyensu, inda ya nuna zai yi wannan aiki, ya dauki jigidar harsasai da aka ba shi, kuma a daidai lokacin da suka yi kusa sai ya sake shi ya fadi, ya nuna kamar ya kwace ne. “Kuma suna tsayawa don in dauka sai na tsere a guje ba na tunanin kaya ko wani abu a daji, suka yi ta harbina harsashi yana samun bishiyoyi, amma na ci gaba da gudu har na isa kauyen wasu mutane suka boye ni.
Baba ya ce washegari ya isa gida ya iske mahaifansa da ’yan uwansa a karo na farko bayan shekara biyu. To amma bai ci gaba da zama da su ba, domin kada ya jawo musu matsala, kuma hakan ya tabbata inda ya samu labarin wani kwamandan Boko Haram ya sanya wasu kudi kan duk wanda ya kashe shi. “Don haka na shiga bas zuwa Damboa na shaida wa ’yan banga cewa ina son yin aiki da su,” inji shi.
Iyayensa ma sun firgita inda suka guje daga gidan, suka koma wani kauyen da sai lokaci-lokaci suke iya ganin babban dan nasu.
Baba Goni yana matukar taimaka wa ’yan banga a shingayen duba ababen hawa wajne fallasa ’yan Boko Haram da ya sani ga sauran. Sai dai ya ce abin da ya daga masa hankali a bangaren gwamnati shi ne ya taimaka wajen fallasa daya daga cikin wadanda suka sace shi mai suna Alhaji, inda aka kama shi aka mika ga sojoji, wadanda suka harbe shi a gabansa.
 “Zuwa yanzu nag a tashin hankali a lokuta da dama. Kuma ga alama babu sauki sai kara tabarbarewa lamarin yake. Kullum kara baci yake fiye da gano ’yan matan da aka sace a dajin,” inji shi.

(Mun dauko ne daga jaridar Daily Mail, ta Ingila).