Baba-ojo ya yi gudun gara…

Watsattsaken Baba-Ojo mai gonakin Ottawa ga shugaba Jatau Mai-sa-in-sa ya tayar da guguwa a kasar Haurobiya, musamman jin cewa ya jefa azargagiyar zargi mai karfin karafa kan manufar Shugaba Mai gudun-loko ta tarwatsa kasa. Idan wannan azargagiya ta tabbata ko kuma ta zama zuki ta-male kama kare ka hada shi da zomo, mu dai mun […]

Baba-ojo ya yi gudun gara…

Shugaba Jatau na duba watsattsaken Baba-Ojo da ya aiko masaWatsattsaken Baba-Ojo mai gonakin Ottawa ga shugaba Jatau Mai-sa-in-sa ya tayar da guguwa a kasar Haurobiya, musamman jin cewa ya jefa azargagiyar zargi mai karfin karafa kan manufar Shugaba Mai gudun-loko ta tarwatsa kasa. Idan wannan azargagiya ta tabbata ko kuma ta zama zuki ta-male kama kare ka hada shi da zomo, mu dai mun fasko cewa barewa ba za ta yi famfalaki ba, danta ya yi tatakin jinjiri.
Baba-Ojo shi ne uban goyon Shugaban Gudun-loko, don haka duk lokom da aka ja Haurobiyawa aka jibge su, kaga su zargi kowa sai mai gonakin Ottawa. Kuma duk wata ta’asa da Haurobiyawa suka ga Jatau Mai sa-in-sa na tafakawa cikin kwanon tasar sa, babu wanda ya nusar da shi illa  uban goyonsa. Bisa wannan dalili nike nusar da ’yan makaranta cewa Mai gonakin Ottawa ya yi gudun gara a wajen neman gararumar kankame ragamar mulkin Haurobiya. Ya nada Shugaba ’Yar’bishiya bai bi soyewar zukatan ubangidansa ba. Don haka ya yi kutu-kutun ganin Jatau ya dare bisa karaga don ya rika juya shi kamar waina.
Kada in mayar da ku baya a karatun jakin-dawa da na-gida, sanin kowa ne an nusar da Baba-Ojo laulayin da Marigayi ’Yar’bishiya ke fama da shi, shi kuma ya ja daga kan cewa matukar ba shi aka yi wa dauki-dora. Wannan manufa ta Baba-ojo kun ga inda ta kai al’umma, kusan kowa na rusa kuka. Arewatawa ba ku kadai ke korafin kan yadda ake walagigi wajen jan ragamar mulkin Haurobiya ba.
Maganar kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma, wannan lamari ne da ya zama ‘ruwan dare da rana’ a zamanin mulkin Baba-ojo; kisan gilla ga masu wasan Samson-siya-siya a dama-dama-da-kurda-kurdar siyasar Haurobiya. Rikicin Hauren-Danja na bunburutu buruntun wawason tunkuza ba bakon al’amari ba ne a wajen Haurobiya. Hasali ma, yanzu Mace-Da-zane ta daure wa samartarkar kusu gindin zama; kodayake ita ma ‘Babbar Budurwar Jaba ce,’ wajen wawason damin Hauro, tunda a karkashin jagorancinta ne Masanin Sisi-da-sisi ya fasa kwai kan yadda aka yi wa tiren-taliya madambaci zari-ruga.
Ga Tumbin-wulli, Shugaba Majalisar wakilan rafkiya, har ya rafko manufar Gudun-loko, inda ya yi nuni da cewa Shagaban Haurobiya ke daure wa kwashi-kwaraf gindin zama. Wannan batu nasa, ai na ingarman karfen karfa ne, domin har yau Haurobiyawa bas u san inda aka sa gaba ba, ballanta a san matsayin Santala kwaiduwa, wadda ta rarike lalitar ma’aikatar kula da sufurin tsuntsaye saman Haurobiya.
Haurobiyawa kuna da labarin an wanke Baudadden Joji da Aminin-dabo, wadanda suka yi wadaka a tashar kwale-kwalen Haurobiya. Duk irin wadannan ayyukan jirkita hukunci, ba wani abu ba ne illa son rai irin na jiga-jigan jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, da ake aiwatarwa a salon mulkin mulaka’u irin na Jatau Mai Sa-in-sa. Ba kuma wani abu ya sanya ake aiwatar da irin wannan kumbiya-kumbiya ba, illa tarwatsa kasa, tamkar yadda Baba-ojo mai gonakin Ottawa ya yi nuni a cikin watsattsaken da ya aike wa dan rainonsa.
Masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a Farfajiyar Dodorido da ke Amintattar Jaridar Haurobiya, ya kamata ku fasko cewa karon-battar Baba-ojo da shagaban Gudun-loko, wata manufa ce ta karkatar da akalar kwanyarku daga turbar tarairayar al’ummar kasa. A matsayina na direban alli, a wannan farfajiya, ina ganin miyagun al’amuran da aka bijiro da su a cikin watsattsakemn Baba-ojo, tilas mu yunkura wajen bai wa kawunanmu kariya; kowa ya sayi sulken karfen karafa.
Kafin in karkare batutuwana a darasin makaranta, ina ganin wajibi ne ga jaridu da mujallun da ake wallafawa a kasar Haurobiya, musamman Balon-faranti da Faffale dalili da Dalilin –taronsu da Ladarshafi, duk su himmatu wajen neman mafita ga al’umma. A daina baza kalaman batanci Rubabben Abban-titi da Mai karanta Labaran-mako a fadar tsaunin billa ta Asosa ke watso wa al’umma. Asararren-Dokin Bobo da Kansakalin Kuku sun tabbatar wa Haurobiyawa mummunan nufin d ake kunshe a watsattsaken Baba-ojo. don haka sai mu kimtsa.
Mu dai mun san ko bade, ko ba jima, sai an yi ta Aminin siyasar Kanawa, wanda ya taba furta cewa “Haurobiya guda ce, amma kowa ya san gidan mahaifinsa.’ Kuma a zamanin da yake hada-hadar siyasarsa mai alamar dan mabudin alheri, an yi tar era wakar tsinuwa ga ‘barawon adakar kuri’u da mai runon kujera.’ Kowa ya yi Zungur kada a yi zugum, na tuno muku da Sa’adunmu na Zungur. Ku ji gargadi da jan na-zomon mai fasaha Akiliya ‘Saba da samo gaskiya,
Ta fi nisa,
Sarari da boyi ka don kaso bunkasa
Ga gargadi ya zuwa garemu zumanina
Ku karkade kunnuwanku
Ku ji ni zumaina
Ku nan na kurkusa har na Chana da nisa
gargadin da zam mana
ku ji shi  ne sikikim-bakaka tiki kaka kyaf tin kif!
Al’amura dai sun tuke, miyagun da ke son baddala Haurobiya sun kai makura. Idan muka ki yin banga-bangar Bankin-koko, to tabbas za mu yi ta kokawa, tunda mun kawa kokowa da masu wawa.

Sakon makaranta

Malam barka da dawowa daga Tagadas

Assalamu alaikum bayan gaisuwa irin ta masu fuskantar alkibla. Ina yi wa Babban Direban alinmu barka da dawowa daga balaguron da ya yi zuwa birnin Tagadas, da ke Jamhuriyar Niyar-jari. ’yan uwana dalibai, idan kun ari takalmin Malam Tunau. A watan tunawa da murdiyya da ake yi a kasarmu Haurobiya ni da Malam mun yi tattaki zuwa wannan gari na Tagadas. Na ji Malam ya yi batun yadda shorido ta ba su gwale-gwale, amma fa duk da haka al’amarin bai kai yada muka sha ba, a wancan karon ba. A bini a darasi na gaba. Ku dai ku zuba na zomo, domin ku sha labari kamar Kamfanin Reuters. Daga Halliru K. Gogel 08039336748.