Babaganaru ya sabunta kwantaraginsa a Kano Pillars

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Muhammad Babaganaru  zai ci gaba da horar da kungiyar na tsawon shekara guda bayan ya sabunta kwantaragin sa, a kokarin da ake yi na kara karfafa karfin kungiyar wajen tunkarar kakar wasanni ta bana.Shi dai Babaganaru ya karbi aikin horar da Pillars ne ana […]

Babaganaru ya sabunta kwantaraginsa a Kano Pillars
Babaganaru ya sabunta kwantaraginsa a Kano Pillars

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Muhammad Babaganaru  zai ci gaba da horar da kungiyar na tsawon shekara guda bayan ya sabunta kwantaragin sa, a kokarin da ake yi na kara karfafa karfin kungiyar wajen tunkarar kakar wasanni ta bana.
Shi dai Babaganaru ya karbi aikin horar da Pillars ne ana tsakiyar kakar wasan da ta gabata a hannun tsohon mai horar da ‘kungiyar  Okey Emordi wanda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa united. Kano Pillars dai ta kammala  wasannin da ya wuce ne a matsayi na 8 a teburin gasar firimiyar Nijeriya.
Shugaban kungiyar Kano Pillars Alhaji Kabiru Baita  ya shaidawa Aminiya cewa kungiyar tana neman kara karfin ta ne ta hanyoyi da dama, wadanda suka hada da sayen ’yan wasa da kuma yin tsari mai inganci wanda zai taimaka masu wajen tunkarar kakar wasa ta bana cikin cikakken shiri.  Daga nan sai ya yaba wa gwamnatin Jihar Kano da bangaren masu horarwa da kuma su kansu ‘yan wasan saboda yadda ake hada hannu don ganin an cimma  nasarorin da ake bukata.
Su ma magoya  bayan kungiyar da sauran masu sha’awar wasan kwallon kafa dake bin  kungiyar  ta Kano Pillars, sun bayana cewa  bisa yadda kungiyar ke shirin tunkarar gasar ta bana akwai kyawawan alamun cewa kwalliya za ta biya kudin sabulu.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa