Baballe Hayatu: Babu soyayya tsakanina da Sadiya Gyale
Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Baballe Hayatu ya ce babu batun soyayya tsakaninsa da jaruma Sadiya Muhammad (Gyale) sai dai mutunci.Jarumin ya bayyana haka ne a lokacin da kafar sadarwa ta Kannywoodscene ta yi hira da shi a makon jiya. An dade ana yada jita-jitar jarumin ne zai auri Sadiya Gyale har aka rika cewa shi […]
Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Baballe Hayatu ya ce babu batun soyayya tsakaninsa da jaruma Sadiya Muhammad (Gyale) sai dai mutunci.
Jarumin ya bayyana haka ne a lokacin da kafar sadarwa ta Kannywoodscene ta yi hira da shi a makon jiya.
An dade ana yada jita-jitar jarumin ne zai auri Sadiya Gyale har aka rika cewa shi ne ya hana ta fim, jita-jitar da jarumin ya karyata, inda ya ce akwai kyakkyawar alaka da kyautattawa a tsakaninsu.
Ya ce ranar da ya fi jin dadin a rayuwarsa ita ce ranar da ya je Makka, ya ce manyan abokansa a indostiri su ne Ali Rabi’u Ali da Saima Muhammad da Sadiya Gyale da Rabi’u HRB da Fati Bararoji .
Ya ce sau da dama za a ga ba ya son magana, inda jama’a ke cewa yana da girman kai, to su sani haka Allah Ya yi shi, ba ya son magana.
“Yadda ake ganina a fim ina masifa, ko daga jijiyar wuya, to a fili ba haka nake ba.” Inji shi.
Ya ce idan ba ya fim kullum yana gida, sannan fim na karshe da ya yi shi ne ‘Surkulle’.