Babangida: Gurgu mai koya wa masu kafa sana’a

Wani gurgu mai suna Ibrahim Garba, wanda aka fi sani da Babangida, ya ce duk da lalular rashin kafa da yake fama da ita yana da akalla matasa 12 masu kafa karkashinsa da yake bai wa horo kan gyaran talabijin da rediyo da aikace-aikacen sanyawa da gyaran tauraron dan Adam, wato Satellite.Matashin, dan asalin Jihar […]

Babangida: Gurgu mai koya wa masu kafa sana’a
Babangida: Gurgu mai koya wa masu kafa sana’a

Wani gurgu mai suna Ibrahim Garba, wanda aka fi sani da Babangida, ya ce duk da lalular rashin kafa da yake fama da ita yana da akalla matasa 12 masu kafa karkashinsa da yake bai wa horo kan gyaran talabijin da rediyo da aikace-aikacen sanyawa da gyaran tauraron dan Adam, wato Satellite.
Matashin, dan asalin Jihar Kaduna, yana gudanar da sana’arsa ne da kuma ba da horon  a shagonsa da  ke unguwar Mu’azu a yankin karamar Hukumar Kaduna ta Kudu cikin jihar Kaduna.  A lokacin zantawarsa da Aminiya, ya ce albarkacin sana’arsa, wadda ya shafe shekara takwas yana gudanarwa ya samu ci da sha da tufafi da tallafawa iyaye da kuma abokan arziki. Babangida ya bayyana cewa ya rasa kafafunsa biyu ne a shekarar 2007 sanadiyyar ciwon Sikila da yake fama da shi.
Ya ci gaba da cewa: “Ina fitowa bakin sana’a kullum daga safiya zuwa marece. Kuma nakan yi aikin sanya Satellite ko talabijin din bango a gidaje amma tun daga lokacin da wannan lalurar ta same ni, ba na  iya yin hakan da kaina sai dai na umarci yaran da muke aiki tare da su. Idan kuma suka yi kuskure sai na yi masu gyaran da ya dace. Akwai kuma lokuta da nake turasu su je aikin su kadai daga nan har zuwa Abuja. Wasu da farko idan suka ganin sukan yi tunanin ba zan iya wannan aikin ba, amma bayan sun ba ni dama sai ka ga sun nuna gamsuwa da akina.” Inji shi.
Banbangida ya ce an haife shi ne a shekarar 1989, ya halarci makarantar firamaren Ahmad Umar da ke unguwar Mu’azu. Ya kuma kammala Kwalajen tunawa da marigayi Sheikh Abubakar Gumi bangaren Islamiyya a shekarar 2003. Ya ce ba shi da wani buri da ya wuce na ya yi aure. A karshe kuma ya yi kira ga matasa da su tashi tsaye domin neman na kansu saboda ta haka ne kawai za su tsira da mutuncinsu a idon al’umma.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno