Babangida ya yi gargadi kan sanya soja cikin siyasa

Tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi gargadin cewa duk wani yunkuri da za a yi don sanya sojoji a cikin harkar siyasa ba zai zame alheri ga kasar nan ba. Janar Babangida yana mayar da martani ne kan cece-kucen da ake yi kan takardar kamala sakandare ta Janar Muhammadu Buhari, inda ya […]

Babangida ya yi gargadi kan sanya soja cikin siyasa
Babangida ya yi gargadi kan sanya soja cikin siyasa

Tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi gargadin cewa duk wani yunkuri da za a yi don sanya sojoji a cikin harkar siyasa ba zai zame alheri ga kasar nan ba.

Janar Babangida yana mayar da martani ne kan cece-kucen da ake yi kan takardar kamala sakandare ta Janar Muhammadu Buhari, inda ya ce, “zai zamo babban hadari a yi hakan.”
Ya ce, babu ta yadda za a yi Janar Buhari ya kai har matsayin Janar na soja ba tare da yana da takardar sakandare ba. Ya ce rundunar sojan Najeriya wata cibiya ce da take tabbatar da tantance takardun ilimin dukkan jami’anta da yi musu horo da sake horar da su. Don haka ya kadu kan yadda muhawara ta yi zafi a kan batun, inda ya bukaci wadanda suke da korafi su tafi kotu.
Ya yi gargadin cewa bai kamata a zubar da mutuncin rundunar soja ba, domin a ra’ayinsa har yanzu cibiya ce ta hadin kan Najeriya, kuma tana damuwa da neman ilimi a tsakanin ’ya’yanta.
Ya ce, “Rundunar soja wata hukuma ce da ta yi imani da yawaita neman ilimi da samun horo. Za ka samu horo a Kwalejin Manyan Hafsoshi. Bayan shekara daya ka sake zuwa wani horo na musamman a kowane fanni. Wata cibiya ce da ta damu da neman ilimi a tsakanin ’ya’yanta koda a lokacin yaki ne. Rundunar soja takan bukaci ka kasance samun horo a fagen yaki da neman ilimi. Hasali ma rundunar soji ne ta fi kowace cibiya ba da horo neman ilimi da kuma ladabi muhimmanci, domin babu wani jami’i da za a kara wa girma zuwa mukami na gaba ba tare da wata takardar karatu ta baya, kuma ya ci jarrabawar wata takarda da ake bukata.”
Don haka ya gargadi ’yan siyasa da su guji tsoma sojoji a cikin siyasa, inda ya ce duk wani yunkuri na yin haka zai kasance hadari ga rundunar da kuma kasar nan.
“Rundunar soji ta kasance cibiya ta hadin kai. Kuma ba zan goyi bayan duk wani shiri na tsoma sojoji cikin siyasa ba,” inji shi.
Ya ce yana da yakinin rundunar sojojin za ta kauce wa fadawa cikin tarkon ’yan siyasa.
“Wannan ba wani abu ba ne, face siyasa. Ina ganin wadanda suke da korafi sun san abin da ya kamata su yi. Duk wanda yake jin ba a yi masa daidai ba, sai ya tafi kotu, ya bari kotu ta yi hukuncin da zai warware komai,” inji shi.