Babayo Gamawa ne zai iya kai PDP tudun-mun-tsira
Shugaban kungiyar Wayar da kan Matasan kofar Wambai a garin Bauchi, Malam Abdulsalam El-Nafati ya bukaci Jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi ta yi adalci ga dukkan wadanda suka nuna bukatar tsayawa takarar Gwamna Jihar a zaben shekara ta 2015, inda ya ce adalci ne babban sinadarin kawo zaman lafiya a tsakanin al’umma, musamman a wannan […]
Shugaban kungiyar Wayar da kan Matasan kofar Wambai a garin Bauchi, Malam Abdulsalam El-Nafati ya bukaci Jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi ta yi adalci ga dukkan wadanda suka nuna bukatar tsayawa takarar Gwamna Jihar a zaben shekara ta 2015, inda ya ce adalci ne babban sinadarin kawo zaman lafiya a tsakanin al’umma, musamman a wannan lokaci da jam’iyyar ke fuskantar babban kalubale a zaben Gwamnan Jihar.
Malam Abdulsalam El-Nafati ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa, inda ya ce daga cikin masu neman Jam’iyyar PDP ta ba su tikitin tsaya mata takarar Gwamna Sanata Babayo Gamawa ya fi sauran ’yan takarar cancanta. “Domin shi ne wanda aka yi imanin zai iya kai jam’iyyar tudun-mun-tsira a zaben badi. Amma idan shugabannin Jam’iyyar suka yi dauki dora tabbas PDP za ta fada cikin mawuyacin hali a dukkan kananan hukumomin jihar 20,” inji shi.
Ya shawarci matasa ’yan siyasa su cigaba da yayata manufofin alheri na Sanata Babayo domin jama’a suna ganin irin gudunmawar da yake bayarwa wajen inganta rayuwar matasan jihar.