Babban Bankin Najeriya ya kara wa’adin mallakar mafi karancin jarin fara canjin kudi

Babban Bankin Najeriya ya kara wa’adin mallakar mafi karancin fara canjin kudi daga 15 zuwa 31 ga wannan watan. Daraktan bankunan da ake ajiye hade da lura da kudaden canji Kebin Amugo ya bayyana haka a wata sanarwar da ya fitar. Ya ce: “Bayan zama da aka yi tsakanin Babban Bankin Najeriya da kuma mu, […]

Babban Bankin Najeriya ya kara wa’adin mallakar mafi karancin jarin fara canjin kudi
Babban Bankin Najeriya ya kara wa’adin mallakar mafi karancin jarin fara canjin kudi

Babban Bankin Najeriya ya kara wa’adin mallakar mafi karancin fara canjin kudi daga 15 zuwa 31 ga wannan watan.
Daraktan bankunan da ake ajiye hade da lura da kudaden canji Kebin Amugo ya bayyana haka a wata sanarwar da ya fitar.
Ya ce: “Bayan zama da aka yi tsakanin Babban Bankin Najeriya da kuma mu, bankin ya daga wa’adin zuwa 31 ga Yuli, 2014. Za a biya kudin ruwa bayan an ajiye mafi karancin jarin fara canji kudi na Naira miliyan 35, hakan ya danganta da yanayin asusun ajiyar ne.
Ya ce Babban Bankin Najeriya zai daina biyan kudin da ya saba biyan ’yan canjin ga wadanda suka ki cikar ka’idar, sannan zai kwace lasisin ajent dinsu na masu canjin kudi.  
Sai dai duk da wannan karin wa’adin masu  sana’ar  canjin kudi sun koka kan sabuwar dokar da Babban  Bankin Najeriya  ya yi musu na karin kudin jarinsu zuwa Naira miliyan 35 ga wadanda ke da lasisi, amma  wadanda ke neman sabon lasisi kuwa sai ya zuba Naira miliyan 70.
’Yan canjin sun gudanar da taro a Legas, inda  suka  koka  kan wannan karin jarin da aka yi musu.
Shugaban kungiyar ’yan canjin na Najeriya Alhaji Aminu Gwadabe ya ce sun kai kukansu ga Gwamnan Babban Bankin Najeriya Mista Godwin Emefiele kan cewa kashi 85 cikin 100 na masu  wannan sana’ar ba su da  wannan jarin.
Ya ce wa’adin da aka ba su ya yi kadan, suna kuma bakin kokarinsu wajen tsayar da farashin dala da magance samuwar jabun kudi, sannan suna taimaka wajen ci gaban tattalin arzikin kasa.
A karshe ya bukaci babban bankin ya saurari kukensu.
Da  wakilin Aminiya  ya  tuntubi mai magana da yawun Babban Bankin Najeriya  ya ce  an samar  da  wannan sabon tsarin ne domin ganin an tsarkake harkokin  tattalin  arzikin  kasa, kuma  batun ’yan canji  babu  shakka  sun gana da hukumar  bankin  kuma  an saurari  kokensu,  amma  har  yanzu  ba  a  zauna  a kan  maganar  ba.