Babban bankin Najeriya ya nusar da masu amfani da bankuna a kan hakkokinsu

Sashen kare hakkin masu amfani da bankuna na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce, a bara ne suka fara gudanar da shirin wayar da kan jama’a dangane da matsalolin da suke fuskanta tsakaninsu da bankunan kasuwanci da suke danne hakkin masu hulda da su. Shirin da aka faro daga wasu jihohin Arewa a bara ya […]

Babban bankin Najeriya ya nusar da masu amfani da bankuna a kan hakkokinsu
Babban bankin Najeriya ya nusar da masu amfani da bankuna a kan hakkokinsu

Sashen kare hakkin masu amfani da bankuna na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce, a bara ne suka fara gudanar da shirin wayar da kan jama’a dangane da matsalolin da suke fuskanta tsakaninsu da bankunan kasuwanci da suke danne hakkin masu hulda da su. Shirin da aka faro daga wasu jihohin Arewa a bara ya tilasta wasu bankuna biyan Naira miliyan dubu 14 da dari 6 (N14.6bn) ga musu hulda da su, bayan kararrakin da jama’a suka rika shigarwa daga shekara ta 2010 zuwa watan Mayun da ya gabata.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin Mataimakiyar Darakta a sashen kare hakkin jama’a na babban bankin, Hajiya Khadijat Kazeem, wacce ta jagoranci wasu manyan jami’an bankin a taro da ’yan jarida a Ibadan, a ranar Litinin, a inda aka kaddamar da irin wannan shiri karo na biyu da zai kunshi jihohin Kudu maso Yamma.
“Daga yanzu kofa a bude take ga duk wanda wani bankin kasuwanci ya danne hakkinsa ya kai kara zuwa wannan sashen kare hakki na CBN, za mu tabbatar da share hawayensa, ba kamar yadda wasu mutane suke cewa sun bar wa Allah ba, saboda rashin sanin hanyar kwatar hakkinsu”. Inji ta.
Dangane da matsalolin da suka fuskanta daga bara da aka fara gudanar da wannan shiri, sai ta ce, “Da yawa mutane suna rububin karbar bashin kudi daga bankuna ba tare da sanin yawan kudin ruwa da za a biya ba. Wannan babbar matsala ce da muka tashi tsaye wajen wayar da kan mutane kan ta, kuma mu sanya su hanya mai sauki da za su magance ta. Kuma akwai wasu shiri da babban bankin yake fitowa da su domin amfanin jama’a, amma abin bakin ciki mutane suna dari-dari da rungumar wadannan tsare-tsare. Saboda haka muka tashi tsaye wajen wayar da kan mutane masu hada-hadar kudi da bankunan kasuwanci domin su ci moriyar shirin”.
Hajiya Khadijat ta ce duk da irin wadannan matsaloli sashen ya fuskanta, zuwa yanzu, sai godiya, domin mutane sun fara fahimtar muhimmancin wannan sashe.
A rana ta biyu ne aka gudanar da wani taro a zauren Cibic Centre da ke Ibadan, wanda ya samu halartat dukkan masu ruwa-da-tsaki da suka danganci hada-hadar kudi da bankunan kasuwanci.