Babban Bankin Najeriya ya shawarci matasa su daina almubazzaranci

A bisa tsarin Babban Bankin Najeriya (CBN) na taimaka wa matasa dangane da yadda za su rika kashe kudadensu ne, babban bankin ya shawarci matasa su da daina almubazzaranci, sannan su rika ajiyar kudi a bankuna.Hajiya Umma Dutse wadda darakta ce a Babban Bankin Najeriya ta ba matasan shawarar a lokacin da take yi wa […]

Babban Bankin Najeriya ya shawarci matasa su daina almubazzaranci
Babban Bankin Najeriya ya shawarci matasa su daina almubazzaranci

A bisa tsarin Babban Bankin Najeriya (CBN) na taimaka wa matasa dangane da yadda za su rika kashe kudadensu ne, babban bankin ya shawarci matasa su da daina almubazzaranci, sannan su rika ajiyar kudi a bankuna.
Hajiya Umma Dutse wadda darakta ce a Babban Bankin Najeriya ta ba matasan shawarar a lokacin da take yi wa daliban yankin Babban birnin tarayya Abuja jawabi yayin taron makon Global Money a ranar Talata.
Ta jaddada cewa babbar hanya wajen inganta rayuwar yara ita ce a nuna musu yadda za su kashe kudinsu a kan hanyar da ta dace, sannan a fahimtar da su illar almubazzaranci.
Hajiya Umma wadda Hajiya Khadijah Kasim ta wakilta ta ce: “CBN ya fito da wani shiri na ilimantarwa don wayar da kan mutane kan abubuwan da suka kamata su saya, da kuma yadda za su rika kashe kudinsu ba tare da almubazzaranci ba, sannan za su ilimantar da ’yan Najeriya dangane da yadda za su zabi abubuwan da suke so a lokaci mafi dacewa.
“Wannan tsarin zai fi amfanar matasa, domin za su fahimci mene ne amfanin yin tattali da hannun jari da kuma yadda za su samu ilimin kashe kudadensu ba wai sai sun tsufa ba.” Inji ta.