Babban Bankin Najeriya zai cusa ilimin sarrafa kudi a manhajar makarantu
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana aniyarsa ta bullo da dabarun koyar da ilimin sarrafa kudi a manhajar makarantun Najeriya, a kowane mataki na ilimi, ta yadda za a warware matsalar wannan bukata da al’umma ke fama da ita.Gwamnan Babban Banki, Malam sanusi Lamido Sanusi ya bayyana wannan manufar, a wajen taron kungiyar dalibai da […]

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana aniyarsa ta bullo da dabarun koyar da ilimin sarrafa kudi a manhajar makarantun Najeriya, a kowane mataki na ilimi, ta yadda za a warware matsalar wannan bukata da al’umma ke fama da ita.
Gwamnan Babban Banki, Malam sanusi Lamido Sanusi ya bayyana wannan manufar, a wajen taron kungiyar dalibai da ke kokarin bunkasa harkokin kafa masana’antu (SAGE) na bana, inda suka bayar da kofin duniya, tare da shirya walimar cin abinmcin dare.
Sanusi wanda ya samu wakilcin Mista Paul Ekluhaiwe, Daraktan sashin bunkasa dabarun sarrafa kudi na babban bankin ya ce, “Saka jari ne a bunkasa matasa masu kokarin kafa masana’antu, a matsayinsu na shugabannin gobe wadanda za su rika juya akalar tattalin arziki, wannan ba bin bukata ce kawai ba, har ma ya zama dole a kara kwazo a kan ala’amarin.”
Gwamnan ya ce Babban Bankin ya himmatu wajen hadin gwiwa da tallafa wa shirye-shirye irin na kungiyar dalibai ta SAGE, wadda za ta samar da manyan masu kafa masana’antu, don warware bukatun al’umma a fadin duniya.