Babban basaraken Jihar Taraba ya mutu
Basaraken ya mutu ne bayan shafe shekara 45 yana mulki.
Babban basaraken Jihar Taraba, kuma Aku Uka na Wukari, Dokta Shekarau Agyo ya mutu.
Marigayin, wanda shi ne ‘Sarkin Jukunawa’ ya mutu yana da shekara 84 a duniya.
- Najeriya na dab da fuskantar karancin iskar da mutane ke shaka – Masani
- APC ta lashe dukkan kujerun Ciyamomi da Kansiloli a zaben Filato
Wakilin Aminiya ya jiwo cewa Sarkin mai daraja ta daya kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Taraba ya mutu ne ranar Asabar a fadarsa dake Wukari bayan yayi fama da rashin lafiya.
Dokta Shekarau Agyo dai ya dare kan karagar mulki ne a watan Agusta na shekarar1976, ya shafe kimanin shekara 45 kenan a kan gadon mulki.
Wata majiya daga gwamnatin Jihar ta shaida wa Aminiya cewa a al’adance, Gwamnan Jihar ne kawai zai iya bayar da sanarwar mutuwar Sarkin a hukumance bayan an kammala wasu al’adu kamar yadda yake kunshe a al’adun ’yan kabilar ta Jukun.